An gano gawar yaro ɗan shekara huɗu da ya ɓace a Abuja, an yanke sassan jikinsa

An tsinci gawar Eleazar Ishiya, yaro ɗan shekara huɗu da haihuwa da aka bayyana ɓacewarsa kwanakin baya, a Abuja, rahotanni sun ce an gano gawarne wacce a aka cire sassan jikinta a cikin wani rami kusa da Mista Biggs na unguwar Jabi a Abuja.

Wani ɗan uwan yaron, ya ce an sanar da ɓatan Ishiya ne a ranar Juma’a, 3 ga watan Maris a filin bal, Jabi ɗaki biyu.

Wani ganau mai suna Joel Joseph, ya ba da cikakken bayani ya ce, “Lokacin da muka ga gawarsa a cikin ramin, kakarsa ta yi yunkurin shiga ciki amma na riƙe ta na hana ta,sai na shiga cikin ramin inda na tarar da gawar ta riga ta ruɓe.

Harshensa da duburarsa da al’aurarsa aka yanke, yayin da aka cire idanunsa.

KU KUMA KARANTA: Yadda wani ya kashe abokinsa, ya siyar da sassan jikin ga Fasto da Boka kan naira dubu 200

“A bayyane yake cewa waɗanda suka kashe shi matsafa ne, kuma watakila sun jefa shi cikin ramin cikin dare.”

Mahaifiyar yaron ta bayyana Ishaya, a matsayin “mai hankali” kuma ɗan makaranta wanda shi ne ɗaya tilo ɗa a gidan.

Ta ce, “A ranar Juma’ar nan mai ban mamaki, Eleazar ya yi wanka, ya ɗauki kuɗi naira 10 ya siyo kayan alawa a wani shagon unguwa, kuma tun a wannan lokacin ya ɓata.

“Ban damu da mutuwarsa ba, sai dai yadda aka azabtar da shi na matukar damu na, na dangana lamarina ga Allah,” In ji ta.

Ta ce bata san masu aikata laifin ba domin ita bata san abinda ya ke ɓoye ba. Jinin yaron zai bi waɗanda suka kashe shi saboda bai yi masu laifin komai ba.

“Ya kamata su dauki kansu sun riga sun mutu, ba zan iya yin ƙarfin hali don ganin ɓarnar jikinsa ba. Daga baya ne na yi nasarar ganin gawarsa a hotuna.’’In ji mahaifiyar Yaron.


Comments

One response to “An gano gawar yaro ɗan shekara huɗu da ya ɓace a Abuja, an yanke sassan jikinsa”

  1. […] KU KUMA KARANTA: An gano gawar yaro ɗan shekara huɗu da ya ɓace a Abuja, an yanke sassan jikinsa […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *