An gano gawar ɗalibar jami’ar Benue da ta ɓata

0
585

Rahotanni sun ce an tsinci gawar wata ɗalibar da ke koyon karatun jarida a Jami’ar Jihar Benue, mai suna Erekaa Naomi Dooshima, kwanaki kaɗan bayan ta ɓace.

Ɗalibar wacce aka fi sani da Affection, ta ɓata ne kwanaki uku da suka gabata kuma duk ƙoƙarin da aka yi na gano inda take ya ci tura.

KU KUMA KARANTA: Yadda aka gano gawar ɗan wasan ƙasar Ghana da girgizar ƙasa ta rutsa da shi a Turkiyya

A cewar wani sakon da ɗan gwagwarmayar Binuwai, Ukan Kurugh ya rabawa manema labarai, ya ce an gano wata waya, katin shaida, da tufafi masu ɗauke da jini da ake zargin na ɗalibar ne a kusa da asibitin Rahama daura da makarantar likitanci a Makurɗi a ranar Talata, 21 ga watan Fabrairu.

A wani ƙarin bayani a ranar Laraba, 22 ga watan Fabrairu, Mista Kurugh ya ce an gano gawarta kuma a halin yanzu jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Benue suna ci gaba da bincike.

Leave a Reply