An dakatar da Hakimi da kansila bisa zargin satar Taransifoma a Gwambe

0
183
An dakatar da Hakimi da kansila bisa zargin satar Taransifoma a Gwambe

An dakatar da Hakimi da kansila bisa zargin satar Taransifoma a Gwambe

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnan jihar Gwambe, Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, ya amince da dakatar da Hakimin Garin Majidadi da ke ƙaramar hukumar Akko, Mohammed Majidaɗi nan take.

Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau juma’a.

Hakazalika, Majalisar ƙaramar Hukumar Akko, bisa dogaro da dokar da ta kafa dokar ƙaramar Hukumar ta Jihar Gombe, ta shekarar 2013, ta kuma sanar da dakatar da Kansila mai wakiltar Kumo ta Gabas, Abdullahi M. Panda.

Dakatarwar ta biyo bayan wasu al’amura da suka faru a baya-bayan nan da suka shafi mutanen biyu, waɗanda rundunar ‘yansandan jihar Gombe ta gurfanar da su a gaban ƙuliya, kuma a halin yanzu suna fuskantar shari’a kan zargin haɗa baki wajen sata da kuma sayar da tiransifoma na al’umma a Garin Majidadi.

KU KUMA KARANTA: ’Yan sanda sun kama wani matashi kan zargin satar kuɗi ta na’urar ATM

Dakatar da mutanen biyu wani mataki ne na kariya don tabbatar da cewa ba a tsoma baki a cikin tsarin shari’a ba.

Gwamna Inuwa Yahaya, wanda ya jaddada ƙudirinsa na tabbatar da doka a kodayaushe, ya bayyana ƙwarin gwiwarsa na cewa adalci zai tabbata, kuma doka za ta yi aiki, ba kawai a kan Majidaɗi da Panda ba, har ma da duk wasu mutanen da aka samu da hannu wajen yin sata.

Leave a Reply