An ceto ɗalibar da tayi yunƙurin kashe kanta

Wata mata ɗalibar kwalejin fasaha a jihar Delta ta yi yunƙurin kashe kanta ta hanyar tsalle daga gadar Oghara-Benin inda ta tsunduma cikin kogi.

Rahotanni sun nuna cewa wani matafiyi da abokinsa suna dawowa daga garin Benin, sai suka ga ɗalibar ta yi tsalle daga gadar inda ta faɗa cikin kogin.

Nan take kuma wasu mutane suka faka motocinsu a saman gadar inda suka yi ta buga ƙararrawa kuma wasu mazauna yankin da ke karkashin gadar sun yi hanzarin shiga cikin kogin suka nufi inda matar ta faɗa.

Haka zalika masu motocin sun kira jami’in ‘yan sandan shiyyar Oghara, wanda su ka tattaro mutane zuwa wurin.

KU KUMA KARANTA:Yan sanda sun ceto yarinyar da ƙanwar mahaifiyarta ta kulle a Filato

An kuɓutar da ɗalibar da ta kammala karatunta, kuma an garzaya da ita asibitin koyarwa na Oghara domin kula da lafiyarta.

Duk da haka, ba a iya gano dalilin da ya sa ta yi niyyan kashe kanta ba,mun kasa samun jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar domin jin ta bakinsa kan lamarin har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.


Comments

One response to “An ceto ɗalibar da tayi yunƙurin kashe kanta”

  1. […] KU KUMA KARANTA:An ceto ɗalibar da tayi yunƙurin kashe kanta […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *