An binne gawar Oreoluwa Aina, ‘yar shekara 28 mai yiwa ƙasa hidima da hatsarin jirgin ƙasa da motar Bus ta BRT ta rutsa da ita a Legas, haɗarin da ya afku a ranar Alhamis, 9 ga watan Maris.
Oreoluwa na cikin mutane shida da aka tabbatar sun mutu bayan da jirgin ƙasa ya murƙushe wata motar bas ɗin ma’aikatan gwamnatin jihar Legas a yankin PWD da ke unguwar Ikeja a jihar.
KU KUMA KARANTA: Masu garkuwa sun kashe ɗan bautar ƙasa, bayan karɓar kuɗin fansa
An binne marigayiyar, wanda ke aikin bautar ƙasa a sashen kula da ayyukan karatu na ma’aikatar ilimi ta jihar Legas a Alausa a ranar asabar a makabartar Atan.
Tawagar gwamnatin jihar ƙarkashin jagorancin kwamishinan ilimi, Folasade Adefisayo ta halarci jana’izar.
Haka kuma akwai ‘yan uwan mamaciyar da kuma kodinetan hukumar NYSC ta jihar Legas, Yetunde Baderinwa.
[…] KU KUMA KARANTA: An binne ‘yar bautan ƙasar da ta mutu a haɗarin jirgin kasa a Legas […]
[…] KU KUMA KARANTA: An binne ‘yar bautan ƙasar da ta mutu a haɗarin jirgin kasa a Legas […]