Ministocin ƙasashen wajen Burkina Faso da Mali da Nijar ranar Juma’a sun bayar da shawarar ƙirƙiro tarayyar ƙasashen uku a wani ɓangare na haɗa kan kasashen don su zama a dunƙule wuri ɗaya.
Dukkan ƙasashen uku na ƙarƙashin mulkin soji inda a Mali da Burkina sojoji suka kwace mulki a 2020 da 2022, sannan a Nijar sojoji suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan Yulin da ya gabata.
Tuni dama suka ƙirƙiri wata ƙungiya mai suna Alliance of Sahel States da zummar ƙarfafa tsaro da bunƙasa tattalin arziki a tsakaninsu.
A wata sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar bayan kammala taron kwana biyu a Bamako babban birnin Mali, ministocin harkokin wajen ƙasashen uku sun bayyana cewa “akwai babbar dama ta zaman lafiya da kwanciyar hankali da ƙarfafa diflomasiyya da bunƙasa tattalin arziki idan aka ɗaukaka dangantaka da alaƙa ta siyasa”.
KU KUMA KARANTA: Sojojin Nijar sun soke dokar da ta haramta tafiya ci-rani Turai
“Ministocin… bisa burinmu na kasancewa tarayya da za ta haɗa Burkina, Mali da Nijar muna bayar da shawarar ƙirƙiro tarayya ta shugabannin ƙasashen ƙungiyar Alliance of Sahel States,” in ji sanarwar.
Ministan Harkokin Wajen Mali Abdoulaye Diop ya ce za su mika shawarar ga shugabannin kasashen, waɗanda za su gana a Bamako a wani lokaci da ba a fayyace ba.
Kazalika gwamnatocin sojin ƙasashen uku sun haɗa wata gamayya da za ta tunkari duk wani matsin lamba daga ƙasashen waje game da komawarsu kan turbar dimokuraɗiyyar da kuma magance hare-haren masu ikirarin jihadi da ke addabar ƙasashen.