Connect with us

Ƙasashen Waje

An bayar da shawarar kafa tarayyar ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso

Published

on

Ministocin ƙasashen wajen Burkina Faso da Mali da Nijar ranar Juma’a sun bayar da shawarar ƙirƙiro tarayyar ƙasashen uku a wani ɓangare na haɗa kan kasashen don su zama a dunƙule wuri ɗaya.

Dukkan ƙasashen uku na ƙarƙashin mulkin soji inda a Mali da Burkina sojoji suka kwace mulki a 2020 da 2022, sannan a Nijar sojoji suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan Yulin da ya gabata.

Tuni dama suka ƙirƙiri wata ƙungiya mai suna Alliance of Sahel States da zummar ƙarfafa tsaro da bunƙasa tattalin arziki a tsakaninsu.

A wata sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar bayan kammala taron kwana biyu a Bamako babban birnin Mali, ministocin harkokin wajen ƙasashen uku sun bayyana cewa “akwai babbar dama ta zaman lafiya da kwanciyar hankali da ƙarfafa diflomasiyya da bunƙasa tattalin arziki idan aka ɗaukaka dangantaka da alaƙa ta siyasa”.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Nijar sun soke dokar da ta haramta tafiya ci-rani Turai

“Ministocin… bisa burinmu na kasancewa tarayya da za ta haɗa Burkina, Mali da Nijar muna bayar da shawarar ƙirƙiro tarayya ta shugabannin ƙasashen ƙungiyar Alliance of Sahel States,” in ji sanarwar.

Ministan Harkokin Wajen Mali Abdoulaye Diop ya ce za su mika shawarar ga shugabannin kasashen, waɗanda za su gana a Bamako a wani lokaci da ba a fayyace ba.

Kazalika gwamnatocin sojin ƙasashen uku sun haɗa wata gamayya da za ta tunkari duk wani matsin lamba daga ƙasashen waje game da komawarsu kan turbar dimokuraɗiyyar da kuma magance hare-haren masu ikirarin jihadi da ke addabar ƙasashen.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ƙasashen Waje

Mutumin da ya fi kowa tsallake haɗari a duniya ya mutu

Published

on

Mutumin da ya fi kowa tsallake haɗari a duniya ya mutu

Mutumin da ya fi kowa tsallake haɗari a duniya ya mutu

Daga Ibraheem El-Tafseer

Frane Selak ya kasance wanda ya fi kowa tsallake rijiya da baya a duniya.

A shekarar 1962 ya tsallake haɗarin jirgin ƙasa wanda mutane 17 suka mutu, a 1963 jirgi ya faɗi da shi kowa ya mutu sai shi kaɗai ko ƙwarzane bai yi ba.

A shekarar 1966 motar safa ta lume da su a rafi mutum huɗu sun mutu amma Frane bai samu ko ƙwarzane ba a yayin da a shekarar 1973 motarsa ta kama da wuta ya tsallake rijiya da baya, ya kuma tsallake haɗarin taho mu gama da mota ta yi da shi ya tsira ya kuma lashe yuro dubu ɗari takwas a Caca a shekarar 2003.

KU KUMA KARANTA: Labarin zuwa Hajji mai ban mamaki

Continue Reading

Ƙasashen Waje

Isra’ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza

Published

on

Isra'ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza

Isra’ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza

Isra’ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza, inda ta tilasta wa ɗaruruwan Falasɗinawa tserewa bayan da soji suka kuma ba da umarnin ƙaurace wasu yankuna masu yawan jama’a.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Isra’ila sun ce an yi musayar wuta da dakarun Masar

Waɗanda suka shaida lamarin sun ce an kai hari da dama a ciki da wajen birnin Khan Younis, inda aka hallaka mutane takwas kuma mutane sama da 30 suka samu raunuka, cewar wata majiyar lafiya da kuma ƙungiyar Red Crescent ta Falasɗinawa.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

Farashin man fetur zai ƙaru a watan Yuli a Ghana – COPEC

Published

on

Farashin man fetur zai ƙaru a watan Yuli a Ghana - COPEC

Farashin man fetur zai ƙaru a watan Yuli a Ghana – COPEC

Ƙungiyar Kare Haƙƙin Masu Amfani da Man Fetur a Ghana ta yi hasashen cewa akwai yiwuwar a samun ƙarin farashin man fetur a ƙasar a farkon watan Yulin 2024.

Ƙungiyar ta Chamber for Petroleum Consumers (COPEC) ta ce akwai alamu masu ƙarfi da ke nuna cewa farashin fetur da man dizel da gas zai ƙaru baki ɗaya a gidajen man da ke faɗin ƙasar, kamar yadda kamfanin watsa labarai na ƙasar Ghana ya ruwaito.

COPEC ɗin ta ce za a samu ƙarin farashin ne sakamakon yadda farashin Cedi ɗin a ƙasar ke ƙara karewa idan aka kwatanta da dalar Amurka.

COPEC ɗin ta yi hasashen cewa farashin man fetur ɗin wanda za a rinƙa sayarwa a gidan mai zai ƙaru da kashi 2.17 cikin 100, wanda hakan ke nufin zai ƙaru daga Cedi 14.17 zuwa Cedi 15.20 a duk lita.

Sai kuma farashin dizel ana sa ran ya ƙaru zuwa 15.21 a kowace lita ɗaya, sai kuma na gas ya koma tsakanin Cedi 13.24 zuwa Cedi 14.64 a duk kilo ɗaya.

KU KUMA KARANTA: Ɗan Ghana ya kafa tarihi na rungumar bishiyoyi a duniya

Ƙungiyar ta COPEC ta bayar da shawara ga gwamnatin Ghana da ta yi duk mai yiwuwa domin rage harajin da yake a kan gas ko kuma yin tallafi a farashinsa domin bayar da dama ga ‘yan ƙasar su same shi a farashi mai rahusa.

Ta kuma yi ƙira ga gwamnati da kada ta yi ƙasa a gwiwa wajen dawo da matatar mai ta Tema a kan aiki (TOR) don kaucewa ko kuma rage shigo tattacen man fetur wanda a wani lokacin ake samun gurɓatacce.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like