An bai wa kamfanoni wa’adin yin rajista da CAC a Nijeriya

0
155

Hukumar da ke yi wa Kamfanoni Rajista a Nijeriya (CAC) ta bai wa kamfanonin da ke ƙasar wa’adin yi rajista kamar yadda doka ta tanada idan ba haka ba ta soke lasisinsu.

Shugaban Hukumar Hussaini Ishaq Magaji ne ya bayyana haka ga manema labarai ranar Juma’a a Abuja, babban birnin ƙasar.

Ya ce dokokin ƙasar sun buƙaci duka kamfanonin da ke ƙasar su rika samar da bayanai abubuwan da suka shafe su “ko sauyin adireshi ko sauyin kasuwanci da sauransu, sannan kamfanin ya biya wasu kuɗi da ba su taka kara sun karya ba.”

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Najeriya za ta sake ajiye ‘yan gudun hijira 22,071 a Neja – Ministar jin ƙai

“Doka ta bukaci duk shekara kowane kamfani ya cika ka’idoji. Duk wanda bai cika ba, to doka ta ba hukumar CAC damar cire sunan wannan kamfanin daga tsarinta,” in ji shugaban CAC.

Hussaini Ishaq Magaji ya ce sun bai wa kamfanoni zuwa ranar 31 ga watan Disamba mai zuwa don su tabbatar sun cika ka’idodin da doka ta tana kan kamfanoninsu.

A ƙarshe shugaban ya yi gargaɗi ga “kamfanonin tafiye-tafiye musamman masu yin aikin Umrah da Hajji da kamfanonin hakar ma’adinai da kamfanonin canjin kuɗin ketare da aka yi wa rajista waɗanda ba su gyara takardunsu ba da su yi hakan.”

Leave a Reply