An ɗaure ɓarawon Talabijin shekaru biyu a gidan gyaran hali

0
385

Wata kotun gargajiya da ke Kafanchan a jihar Kaduna ta yanke wa wani matashi ɗan shekara 20 mai suna James Monday hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan gyaran hali bisa samunsa da laifin satar talabijin.

Rundunar ‘yan sandan ta gurfanar da wani tsohon mai laifi a ranar Litinin, bisa laifin shiga gida da sata, saɓanin tanadin sashe na 327 da 270 na dokar laifuka ta jihar Kaduna.

Ɗan sanda mai shigar da ƙara, Isfekta Esther Bishen, ta shaida wa kotun cewa wanda ya shigar da ƙarar, Ezekiel Ɗanladi, ya kai ƙarar ‘yan sanda a ranar 3 ga watan Satumba.

KU KUMA KARANTA: Ɓarawon da kotu ta ɗaure saboda sata ya kuma yin sata jim kaɗan bayan da aka sako shi

Ta ƙara da cewa an kama shi a ranar Litinin bayan da ya je gidan mai ƙarar da ke Ungwan VIO a Kafanchan ya saci TV da kuɗinsa ya kai naira 40,000.

Ɗan sanda mai gabatar da ƙara ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya yi zaman gidan yari bisa irin wannan laifin a shekarar 2021.

Da aka karanta masa tuhumar da ake masa, wanda ake tuhumar ya amsa laifinsa tare da roƙon kotun da ta yi masa sassauci.

A hukuncin da ya yanke, Alƙalin kotun, George Gwani, ya yanke hukuncin zaman gidan yari na watanni shida a ranar Litinin ko kuma tarar Naira 5000 a shari’ar farko da tarar shekara biyu ko naira 30,000 kan tuhuma ta biyu.

Mista Gwani ya ce hukuncin zai gudana ne a lokaci guda.

Leave a Reply