An ƙuɓutar da ‘yan’uwan Nabeeha daga masu garkuwa da mutane

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce jami’an tsaro sun ƙuɓutar da ‘yan matan nan biyar da ke hannun masu garkuwa da mutane bayan ‘yan bindiga sun kashe ‘yar’uwarsu wato Nabeeha Al-Kadriyar.

An sace ‘yan matan shida ne da mahaifinsu ranar 2 ga watan Janairun da muke ciki a gidansu da ke Bwari a Abuja.

Sai dai daga bisani ‘yan bindigar sun saki mahaifinsu sannan suka buƙaci ya nemo N60m a matsayin kuɗin fansa.

Lamarin ya ɗauki sabon salo bayan ‘yan bindiga sun kashe Nabeeha a yayin da wata makusanciyarsu Asiya Adamu take tattara kuɗin fansar bayan ta roki mutane a shafukan sada zumunta.

KU KUMA KARANTA: Pantami ya samo wanda zai biya kuɗin fansa a sako ‘yan uwan Nabeeha da aka sace a Abuja

Sai dai a sanarwar da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Abuja Josephine Adeh ta fitar ranar Asabar da tsakar dare, ta ce jami’ansu da na rundunar sojin Najeriya sun ƙuɓutar da ‘yan matan ‘yan’uwan Nabeeha.

Sanarwar ta ce an gano su ne a kusa da dajin Kajuru da ke Kaduna ranar Asabar da misalin karfe 11:30 na dare.

Ta ƙara da cewa tuni aka kai ‘yan matan gidansu da ke yankin Bwari a birnin na Abuja.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *