An ƙaddamar da gina inda ya rufta a babban masallacin fadar Sarkin Zazzau

0
22
An ƙaddamar da gina inda ya rufta a babban masallacin fadar Sarkin Zazzau

An ƙaddamar da gina inda ya rufta a babban masallacin fadar Sarkin Zazzau

Daga Idris Umar, Zariya

An ƙaddamar da ginin babban masallacin ƙofar fadar Sarkin Zazzau da ke birnin Zariya wanda ya rufta a watanin baya da suka wuce kuma yayi sanadiyyar rasuwar mutane a lokacin.

Shi dai wannan babban Masallacin na garin Zazzau na Sarkin Zazzau Abdulkarimne kuma ya rufta ana tsaka da sallah La’asarne sakamakon ruwan sama mai ƙarfin gaske. Wannan masallaci yana da tarihi sosai.

Bugu da ƙari wannan masallacin tsohon magininanne kuma shahararre, wato mai suna Babban Gwani ya ginashi tun shekaru kusan dari biyu da suka wuce.

Bisa wancan lalura da ta farune masarautar Zazzau bisa jagorancin mai Martaban Sarkin Zazzau Ambassador Ahmed Nuhu Bamalli ta ɗau alwashin rusheshi tsohon ginin don sake saban wani ginin a wannan muhalli.

KU KUMA KARANTA: Ruwan sama a Nijar ya rusa masallaci mai ɗimbin tarihi

Masarautar kasar Zazzau ta ƙaddamar da bukin aza harsashi ginin Sabon masallacin tare da karɓar gudummawa daga wasu manyan mutane

Daga cikin Mayan mutane da suka hallaci taron akawai Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani da kakakin majalisar taraiyya RT honorable Abas Tajuddin da ministan muhalli Alhaji Balarabe Lawal Abas.

An ƙaddamar da ginin masallacin lafiya an tashi lafiya.

Leave a Reply