Amurka ta sake nanata ƙudurinta na tsayawa tsayin daka a fannin tattalin arziƙi da kasuwanci a ƙasashen Afirka.

0
105

Daga Maryam Umar Abdullahi

Da take jawabi jiya a wajen taron kasuwanci da zuba jarin Afrika da aka gudanar a cibiyar taron Eko dake jihar Legas, mai baiwa Amurka shawara kan harkokin kasuwanci Julie LeBlanc, ta ce a shekarar da ta gabata kaɗai, Amurka ta tallafa tare da kammala wasu sabbin yarjejeniyoyin guda 547, waɗanda suka kai kimanin dala biliyan 14.2, wanda ke nuna ƙaruwar kashi 60 cikin 100 na adadin da kuma darajar yarjejeniyoyi da aka cimma idan aka kwatanta da shekarar 2022.

LeBlanc ta ce, ziyarar da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya kai ƙasashen yammacin Afirka ciki har da Najeriya, Cape Verde, Cote d’Ivoire, da Angola, ya nuna aniyar ƙudurin da Amurka ta ɗauka kan Afirka kwanan nan.

“Wannan ziyarar ta ƙarfafa himmarmu wajen inganta haɗin gwiwar tsaro, ayyukan kiwon lafiya, da bunƙasar tattalin arziƙi a yankin.”

KU KUMA KARANTA: Najeriya ta tsallaka zuwa wasa na kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin Afirka

“Gudunmawar da gwamnatin Amurka ta bayar na dala miliyan 160 don tallafawa cinikayya a Nahiyar Afirka ya misalta ƙudurinmu. Manufarmu wannan tallafin, ita ce faɗaɗa cinikayya da kuma tallafawa Mata da Matasa a Nahiyar Afirka.”

LeBlanc ta ci gaba da cewa: “Najeriya tana ɗaya daga cikin manyan ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziƙi a Nahiyar, mun fahimci muhimmiyar rawar da take takawa a kasuwannin yanki da na duniya. Najeriya ta kasance babbar abokiyar cinikayyarmu ta biyu a Afirka.”

“Muna ganin Nijeriya a matsayin babbar shugaba a Nahiyar, kuma babbar abokiyar tarayya wajen ciyar da kyawawan ɗabi’unmu. Abin da ya amfanar da Nijeriya, zai amfanar da Afirka, da ma duniya baki ɗaya.”

Leave a Reply