Amurka da Rasha sun kammala tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin Ukraine a ƙasar Saudiyya

0
24
Amurka da Rasha sun kammala tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin Ukraine a ƙasar Saudiyya

Amurka da Rasha sun kammala tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin Ukraine a ƙasar Saudiyya

Manyan jami’an Amurka da Rasha sun kamala tattauwar sulhun da suka yi a birnin Riyadh a kasar Saudiyya jiya Talata, inda suka tattauna akan samo mafita ga yakin Ukraine, kwanaki gabanin sarki mai jiran gado, Yarima Muhammad ibn Salman ya kira wani taro da shugabannin Misra, Jordan,Qatar da hadadiyar daular Larabawa su tattauna akan martanin kasashen Larabawa ga alkawrin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi cewa zai karbe ikon Gaza.

Tattaunawar 2 da basu da alaka, ya nuna irin rawar da yariman take takawa a yunkurin ganin Trump ya cika alkawarin da yayiwa magoya bayan shi a lokacin gangamin yakin neman zabe na kawo karshen yakin Ukraine da na Gaza.

KU KUMA KARANTA:Ukraine ta yi ƙira ga manyan ƙasashen yamma da su taka wa Koriya ta arewa birki, kan shirin taimaka wa Rasha a yaƙi da Ukraine

A jiya Talata, shugaba Trump ya sake bayyana cewa zai gaggauta kawo karshen yakin.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, jiya Talata yace Amurka tana kokarin ganin an samu mafita adala mai dorewa wajen kawo karshen yakin da Rasha ta shafe kimanin shekaru uku ta na yi a Ukraine, sai dai dole ne Rashar da Ukraine, kowaccen su, ta hakura da wani abu, kafin a iya cimma zaman lafiya.

Rubio ya yi wannan bayanin ne, bayan da shi da sauran manyan jami’an Amurka su ka gana ta tsawon sama da sa’o’i hudu a kasar Saudiyya da Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergy Lavrov da hadiman shi, a wani yunkurin farko na kawo karshen yakin, da kuma inganta dangantakar Amurka da Rasha da ta yi tsami.

Manufar ita ce a kawo karshen wannan tashin hankalin ta hanyar adalci, mai dorewa, wace dukkanin bangarorin da abin ya shafa zasu aminta da ita” inji Rubio ga menema labarai, duk da cewa babu jami’an Ukraine ko na Turai a wurin tattaunawar.

Leave a Reply