Amnesty ta buƙaci gwamnan Kano ya kafa kwamitin bincike kan kashe masu zanga-zanga a jihar

0
38
Amnesty ta buƙaci gwamnan Kano ya kafa kwamitin bincike kan kashe masu zanga-zanga a jihar

Amnesty ta buƙaci gwamnan Kano ya kafa kwamitin bincike kan kashe masu zanga-zanga a jihar

Daga Ibraheem El-Tafseer

Ƙungiyar kare haƙƙin bil-adama ta Amnesty International ta yi ƙira ga gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya gaggauta kafa kwamitin shari’a mai zaman kansa domin binciken kisan da ƙungiyar ta bayyana da na ”ganganci” kan aƙalla masu zanga-zanga 10 a unguwannin Kurna da Kofar Nasarawa.

Cikin wata sanarwa da daraktan ƙungiyar, Isa Sanusi ya fitar, ya ce dole ne kwamitin ya yi aikinsa, ba tare da katsalandan ba, kuma ya zama wajibi gwamnati ta ba shi duk abin da yake buƙata don gudanar da aikinsa.

Ƙungiyar ta kuma ce dole ne a binciki yadda jami’an tsaron Najeriya suka tunkari zanga-zangar, da kuma irin ɓarnar da ”yan dabar” da aka yi zargin hayarsu domin kawo fitina a lokacin zanga-zangar.

KU KUMA KARANTA: Za mu ci gaba da zanga-zanga saboda jawabin Tinubu bai taɓo buƙatunmu ba – Ƙungiyar ‘The Take it Back Movement’

“Rashin gudanar da bincike kan kashe-kashe da lalata dukiyoyi da aka yi a Kano tun daga ranar 1 ga watan Agusta zuwa yau, ka iya kawo tarnaƙi ga bin doka da Oda”

Sanarwa ta ƙara da cewa rashin binciken zai sa ɗabi’ar nan ta rashin hukunta masu laifi ta ci gaba da wanzuwa a ƙasar, kamar yadda dama ba sabon abu ba ne a Najeriya, in ji sanarwar.

An dai samu hatsaniya a lokacin zanga-zangar adawa da matsin rayuwa da aka gudanar a Kano cikin makon nan, inda aka zargi jami’an tsaro da harbe masu zanga-zangar.