Ambaliyar Ruwa: Gidauniyar tunawa da Sardauna ta ba da tallafin naira miliyan 20 a Maiduguri

0
198
Ambaliyar Ruwa: Gidauniyar tunawa da Sardauna ta ba da tallafin naira miliyan 20 a Maiduguri

Ambaliyar Ruwa: Gidauniyar tunawa da Sardauna ta ba da tallafin naira miliyan 20 a Maiduguri

Daga Idris Umar, Zariya

Gidauniyar tunawa da marigayi Sardauna da ke jihar Kaduna ta ba da gudummawar Naira miliyan 20 ga waɗanda ibtila’in ambaliyar ruwa a Maiduguri ya shafa a wannan shekarar.

Darakta Janar na gidauniyar Injiniya Abubakar Gambo Umar, shine ya sanar da bayar da gudummawar a wata sanarwar manema labarai a Kaduna.

Injiniya Abubakar Gambo yace, Gidauniyar ta kaiwa gwamnan Jihar Borno, Umara Babagana Zulum ziyarar jaje a ranar litinin din wannan makon domin nuna alhinnsu dangane da faruwar iftila’in dukiyoyi masu yawan gaske.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Kano za ta gina gidaje kyauta ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa

Shugaban yace sun bayar da gudummawar domin ragewa waɗanda iftila’in ya shafa raɗaɗinin asarar da suka yi.

Akan hakan gidauniyar ta buƙaci hukumomi da shugabannin na Najeriya da ƙasashen waje da su tallafawa waɗanda iftila’in ya shafa domin rage musu raɗaɗin asarar da suka yi yana mai cewa gidauniyar Tana jajanta musu da kuma yi musu addu’oin Hana faruwar lamarin a nan gaba.

Kuma tayi yabo da jinjina ga sauran jihohi da mutane daidaiku da suka bayar da tasu gudummawar.

Leave a Reply