Al’ummar ƙaramar hukumar Ƙiru ta jihar Kano, sun koka kan karyewar gadoji a yankin

0
25
Al'ummar ƙaramar hukumar Ƙiru ta jihar Kano, sun koka kan karyewar gadoji a yankin

Al’ummar ƙaramar hukumar Ƙiru ta jihar Kano, sun koka kan karyewar gadoji a yankin

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Al’ummar Sabon Garin Alhazawa da ke Ƙaramar Hukumar Ƙiru sun koka kan karyewar manyan gadojin su guda biyu da su ka haɗa garin da sauran garuruwa.

Sunusi Dauda Alhazawa, wanda akafi sani da Sunusi Khalifa, ya shaidawa manema labarai cewa lamarin ya jefa su a mawuyacin hali, inda ya ce har ta kai ga ama asarar rayuka sakamakon karyewar gadojin.

A cewar Sunusi, wanda shi ne Sakataren ƙungiyar ci gaban garin Alhazawa, ya baiyana cewa sun jima da matsalar kuma har yanzu ba a kawo musu dauki ba duk da irin kiraye-kiraye da koke-koke da su ke yi.

KU KUMA KARANTA:An sace wata dattijuwa a asibitin Dawanau dake Kano

Ya ce idan damuna ta sauka, ba a iya wucewa ta hanyoyin, inda ya kara da cewa mata masu juna biyu da kananan yara suna shan wahala, inda har rasa rayuka ake yi a lokacin damina.

“Mu na shan wahala. Ka ga idan damina ta yi, to hanyoyin nan ba damar wucewa kuma har rasa rayuka ake yi, musamman mata masu juna biyu.

“Wannan matsala ta dade kuma ya haifarana da durkushewar tattalin arziki sakamakon cewa hatta kayan amfanin gona ma ba ma samun wucewa da su zuwa garuruwan da mu ke makwabtaka da su.


“Mun yi korafi, mun yi kukan, mun yi kira amma shiru. Saboda haka muna kira da babbar murya da a kawo mana dauki,” a cewar Sunusi.

Har ‘ila yau, Sanusi ya kara da cewa alummar Alhazawa sun koka kan lalacewar asibitin garin, lamarin da su ke ganin akwai barazana a harkokin lafiya a gare su.

Leave a Reply