Al’ummar Nijar na maraba da matakin ECOWAS na janye musu takunkumi

0
98

Matakin ɗage wa ƙasashen Mali da Nijar da Burkina Faso da kuma Guinea takunkumin da ƙungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta sanar a ƙarshen taron shugabannin ƙasashen Yammacin Afirka da ya gudana a wannan Asabar 24 ga watan Fabrairu a Abuja ya saka farin ciki a zuciyoyin jama’ar jamhuriyar Nijar.

Sakamakon yadda abin ke kawo ƙarshen yanayin ƙuncin rayuwar da aka shiga yau watanni kusan 7 sanadiyar rufe iyakoki da taƙaita zirga-zirga harakokin kasuwanci da tsinke wutar lantarki.

Koda yake wasu na ganin matakin ya zo a makare kasancewar tuni Mali da Bukina Faso da Nijar suka sanar da ficewa daga ƙungiyar ta ECOWAS, don mayar da hankula ga ƙungiyar su ta AES.

KU KUMA KARANTA:ECOWAS ta janye takunkumin da ta saka wa Nijar

A ɗaya gefe kuwa, wasu ‘yan ƙasar ta Nijar sun buƙaci aje zuwa mataki na gaba, ma’ana a gaggauta sallamar hamɓararren shugaban ƙasa Mohamed Bazoum da mai ɗakinsa, sannan lokaci ya yi da ya kamata hukumomin mulkin sojan Nijar su fitar da jadawalin ayyukan gwamnatin riƙon ƙwarya don bai wa ‘yan siyasa damar soma shirye-shiryen zaɓen dimokuraɗiyya.

Kamfanoni da dama sun tafka asarar ɗimbim kuɗaɗe a sanadiyar takunkumin da CEDEAO ko ECOWAS ta ƙaƙaba wa Nijar, saboda haka wasu ‘yan ƙasa ke fatan ganin an fara maganar biyan diyya.

Kawo yanzu mahukuntan jamhuriyar ta Nijar ba su bayyana matsayinsu ba dangane da shawarwari da taron na Abuja ya tsayar.

Leave a Reply