Al’ummar jihar Ondo sun kammala kaɗa ƙuri’a a mafi yawan rumfunan zaɓe

0
37
Al’ummar jihar Ondo sun kammala kaɗa ƙuri'a a mafi yawan rumfunan zaɓe

Al’ummar jihar Ondo sun kammala kaɗa ƙuri’a a mafi yawan rumfunan zaɓe

A ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba, 2024 ne al’ummar jihar Ondo suka zaɓi sabon gwamnan da zai jagorance su.

Gabanin zaɓen, hukumar zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta tantace jam’iyyun siyasa 18 da za su fafata a zaɓen. Za a kaɗa ƙuri’a a rumfunan zaɓe 3,933 na kananan hukumomin 18 dake jihar.

Mutane 2,053,061 ne suka yi rajistar zabe a jihar. Hukumar INEC ta ce za ta tura na’urar tantance masu kada kuri’a (BVAS) da bututun bayanai na (IReV) don gujewa tafka magudi.

KU KUMA KARANTA:Zaben Ghana: Sojin ƙasar sun yi ɗamarar samar da zaman lafiya

A ranar Juma’a ne alkalan zaben suka fara rabon muhimman kayayyaki ga kananan hukumomin inda suka ce a shirye suke domin gudanar da zaben.

An baza ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da tsaro a jihar.

Gwamna mai ci Lucky Aiyedatiwa wanda ya gaji marigayi Gwamna Rotimi Akeredolu bayan rasuwar sa a karshen shekarar da ta gabata yana takara a zaben.

Sai kuma Babban abokin takarar sa Ajayi Agboola na jam’iyyar PDP, da kuma sauran ‘yan takara.

Leave a Reply