Al’ummar Jibiya sun nemi agajin Tinubu da Raɗɗa kan takurawar da Kwastam suke yiwa ‘yan kasuwa a hanyar

0
592

Al’ummar garin Jibiya ta jihar Katsina sun nemi agaji daga Tinubu, Raɗɗa, Shugaban Kwastam, DSS, kan matsin lambar da Kwastam ke yiwa ‘yan kasuwa akan hanyar Jibiya.

Al’ummar ƙaramar hukumar Jibiya da ke jihar Katsina a Najeriya sun bayyana damuwarsu kan yadda jami’an hukumar kwastam da sauran jami’an tsaro ke matsa lamba kan ‘yan kasuwa a lokacin jigilar kayayyakin amfanin yau da kullum a hanyar Katsina zuwa Jibiya.

A yayin wani taron manema labarai da ƙungiyar ‘Jibiya People’s Forum’ ta shirya a ranar Alhamis, 1 ga watan Yuni, 2023, shugaban k
ƙungiyar, Alhaji Gide Ɗahiru da sakatarensa, Malam Bishir Lawal, sun bayyana cewa “motocin da ke ɗauke da kayayyaki daga Katsina zuwa Jibiya kamar masara. Alkama, gishiri, suga, gari, dawa, wake, taki, siminti, rogo, masara, gero, kayan ɗaki da dai sauransu, direban mota sai sun kashe kusan Naira dubu 75,000 ga kowace mota J5, sannan su kashe kusan Naira dubu ɗari (100,000) kan kowace babbar mota.”

“Haka kuma motocin da ke ɗauke da ƙarafa daga hanyar Jibiya zuwa Katsina suna kashe kimanin Naira dubu 160,000 wanda ba haka yake a sauran ƙananan hukumomin jihar ba.” inji su.

Wani ɗan kasuwa, Alhaji Sama’ila Mai Masara, ya ce idan suka sayi kayayyakin amfanin yau da kullum daga wasu sassan Najeriya, jami’an tsaro ba sa yi musu barazana sai hanyar Katsina zuwa Jibiya.

“Hakan ya jawo tsadar kayayyaki kuma hakan ya jawo durƙushewar jarin ‘yan kasuwa da dama, kuma hakan ya jefa al’ummar yankin cikin wani yanayi na taɓarɓarewar tattalin arziƙi da ba a taɓa ganin irinsa ba.

Alhaji Sama’ila ya ƙara da cewa “mun kai ƙararmu ga masu riƙe da muƙaman siyasa da sarakuna da sauran hukumomin gwamnati amma abin ya ci tura.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Katsina Dikko Raɗɗa, ya naɗa sakataren gwamnati da wasu da dama

Shugaban ƙungiyar Jibiya People’s Forum Alhaji Gide Ɗahiru da sakatarensa Malam Bishir Lawal sun bayyana cewa rashin samun kayayyaki daga ‘yan kasuwa zuwa Jibiya ya jefa iyalan ma’aikata da dama cikin fatara da yunwa, wasu kuma sun yi ƙaura zuwa wasu sassan jihar. Ƙasar, yayin da wasu suka koma ƙasashen ƙetare domin nemawa kan su mafita.

A ƙoƙarin ƙungiyar Jibiya People’s Forum da sauran ƙungiyoyin farar hula na kai ɗauki ga al’ummar ƙaramar hukumar, suna ƙira da babbar murya ga Shugaban Tarayyar Najeriya, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa, Darakta Janar na Ma’aikatar (DSS) ta Jiha, Babban kwamandan Hedikwatar DSS na Ƙasa da ke Abuja, Hafsan Hafsoshin Soja, sashe na huɗu da ke Katsina, jihar Katsina da kuma babban jami’in hukumar kwastam ta ƙasa (NCS) dake Abuja, da su yi duk mai yiwuwa wajen ganin an magance matsalolin da al’umma ke fuskanta ciki har da matsalar rashin tsaro.

Kimanin kilomita 40 ne daga birnin Katsina zuwa Jibiya, akwai shingayen binciken jami’an kwastam da sauran jami’an tsaro daban-daban a kan titin aƙalla 30, kuma garin Jibiya na ɗaya daga cikin manyan iyakokin Najeriya da ke kan iyaka da Jamhuriyar Nijar.

Leave a Reply