Connect with us

Rasuwa

Allah Ya yi wa tsohuwar jarumar Kannywood, Fati Slow rasuwa

Published

on

Allah Ya yi wa tsohuwar jarumar Kannywood, Fati Slow rasuwa

Allah Ya yi wa tsohuwar jarumar Kannywood, Fati Slow rasuwa

Wannan na cikin wani sako da tsohuwar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa, Mansura Isah ta wallafa a shafinta na Instagram da safiyar ranar Talata.

Mansura ta wallafa cewar “Innalillahi wainna illahi raji’un, Allah Ya yi wa Fati Slow rasuwa.

“Allah Ya jikanta, Allah Ya yi mata rahama, ameen.”

KU KUMA KARANTA: Rasuwar Saratu Giɗaɗo ta girgiza masana’antar Kannywood

Mansura ta ce tsohuwar jarumar ta rasu ne a wani gari Abasha da ke kusa da Sudan, kuma tuni aka yi jana’izarta a can.

A cewarta yanzu haka ana zaman makokinta a gidansu da ke Unguwa Uku a Jihar Kano.

Fati Slow a baya ta fice a harkar fim din Hausa kafin daga bisani ta yi ɓatan-dabo.

Jarumar a shekarar da ta wuce ta sha tayar da ƙura a kafafen sada zumunta.

Tuni ‘yan masana’antar Kannywood da sauran al’ummar Musulmi suka shiga yi mata addu’ar samun rahama da Ubangiji.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ƙasashen Waje

Iran ta tabbatar da mutuwar shugaban ƙasar, Ebrahim Ra’isi, a hatsarin jirgin sama

Published

on

Iran ta tabbatar da mutuwar shugaban ƙasar, Ebrahim Ra’isi, a hatsarin jirgin sama

Daga Ibraheem El-Tafseer

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta tabbatar da cewa, Shugaban Ƙasar Ebrahim Raisi ya rasu bayan wani hatsarin jirgin helikwafta da ya rutsa da shi.

Wani jami’in gwamnatin ƙasar ta Iran ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters, cewa shugaban ƙasar ya rasu ne tare da ministan harkokin waje Hossein Amirabdollahian.

Har ila yau daga cikin waɗanda suka rasu a hatsarin, akwai Gwamnan Gabashin Lardin Azerbaijan, Malek Rahmati da Limamin Tabriz, Imam Mohammad Ali Alehashem da shugaban jami’an tsaron tawagar da babban dogara shugaban ƙasar da shugaban ma’aikatan jirgin da kuma matuƙa jirgin su biyu.

KU KUMA KARANTA: Jirgi mai sauƙar ungulu ɗauke da shugaban ƙasar Iran Ra’isi, ya faɗi

Ana sa ran a rantsar da mataimakin shugaban ƙasar ta Iran na farko, Mohammad Mokhber a matsayin sabon shugaban ƙasa.

Masu hasashe dai na bayyana fargabar mutuwar Shugaba Raisi na iya sake jagula rikicin gabas ta tsakiya wanda Isra’ila ke ci gaba da kashe Falasɗinawa tun bayan ƙaddamar da hare-haren a yankin Gaza, saboda nuna ɗan yatsa da za a yi ga Isra’ila da aminiyarta Amurka saboda yadda sa-in-sa ta ɓarke a tsakanin Iran da Isra’ila bayan harin da Isra’ila ta kai wa ƙaramin ofishin jakadancin Iran a Siriya da ya yi sanadiyyar mutuwar wasu manyan hafsoshin sojin Iran.

Ita ma Iran ta mayar da martani ta hanyar ƙaddamar da hare-hare da jirage marasa matuƙa kimanin 300 inda suka lalata wasu wurare na sojoji a Isra’ila yayin da kuma Ingila da Amurka suka yi iƙirarin sun tare galibin jirage da makaman da Iran ta harba a kan Isra’ila.

Continue Reading

Labarai

An yi jana’izar marigayi Sarkin Tikau a fadarsa (Hotuna)

Published

on

Daga Ibraheem El-Tafseer

Cikin hawaye da jimami aka yi jana’izar marigayi Sarkin Tikau, Alhaji Muhammad Abubakar Ibn Grema, wanda ya rasu ranar Juma’a, a fadarsa da ke Sabon Garin Nangere, Jihar Yobe.

Muhammad, wanda ya rasu yana da shekaru 73, an binne shi a inda aka binne sarakunan da suka gabata na masarautar Tikau.

Babban Limamin Masarautar Tikau Shaikh Adamu Mohammed ne ya jagoranci Sallar jana’izar a fadar da misalin karfe 4:15 na yamma kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, sakataren gwamnatin jihar, Baba Mallam Wali, kakakin majalisar dokokin jihar, Hon. Ciroma Buba Mashio, Sanata mai wakiltar Yobe ta Kudu (Zone B) Sanata Ibrahim Mohammed Bomoi, sarakunan Bade, Damaturu, Katagum, Kaltungo, Gujba, Machina, Jajere, Fune, Ngelzerma da sauran jiga-jigan gwamnati.

Ya rasu ya bar mata uku, ‘ya’ya 23 da jikoki da dama.

Masarautar Tikau na ɗaya daga cikin sarakuna 12 da aka ƙirƙiro a jihar Yobe, wanda marigayi Sanata Bukar Abba Ibrahim ya yi, bayan an ƙirƙiri jihar Yobe a shekarar 1991.

Ya gaji mahaifinsa marigayi Abubakar Grema a ranar 25 ga Yuli, 2001.

KU KUMA KARANTA: Sarkin Tikau na jihar Yobe ya rasu

Marigayi sarki, kafin zamansa Sarki, shi ne Principal na GSS Nangere kuma Hakimin Sabon Garin Nangere, daga nan kuma ya zama Sarkin Tikau. Ya yi mulki tsakanin 2001 zuwa 2024. Bayan zamansa Sarki, ya taɓa zama shugaban jami’ar jihar Yobe (chancellor).

Ɗaruruwan al’umma ne suka yi ɗafifi a fadar cikin cikin jimami da hawaye domin yiwa gawar sarkin bankwana.

Continue Reading

Rasuwa

Sarkin Tikau na jihar Yobe ya rasu

Published

on

Daga Ibraheem El-Tafseer

Da yammacin ranar juma’a ne, Allah ya yiwa mai martaba sarkin Tikau, Alhaji Muhammad Abubakar Grema OON, rasuwa. Mai Tikau ya rasu ne sakamakon doguwar jinya da ya yi fama da ita.

Fadar mai martaba sarkin Tikau tana garin Sabon Garin Nangere da ke ƙaramar hukumar Nangere a jihar Yobe. Ya rasu ne a Asibitin ƙwararru da ke garin Potiskum (Yobe State Specialist Hospital Potiskum).

KU KUMA KARANTA: Ɗan Majalisar Tarayya daga Jigawa ya rasu

Zuwa haɗa wannan rahoto, fadar Mai Tikau ba ta cire sanarwa na lokacin jana’izarsa ba. Amma ana sa ran za a yi jana’izar gobe Asabar a fadarsa da ke Sabon Garin Nangere.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like