Allah Ya yi wa surkar Sarkin Zazzau rasuwa

0
40
Allah Ya yi wa surkar Sarkin Zazzau rasuwa

Allah Ya yi wa surkar Sarkin Zazzau rasuwa

Daga Idris Umar, Zariya

Mahaifiyar mai ɗakin Sarkin Zazzau, Hajiya Habiba, ta rasu bayan gajeruwar rashin lafiya a gidanta da ke Zariya.

Mamaciyar, Hajiya Habiba, ita ce babbar mai ɗakin Sarkin Zazzau mai rasuwa, Alhaji Shehu Idris, wanda Sarki Bamalli ya gaji kujerarsa

Masarautar Zazzau ta sanar da cewa Marigayiya Hajiya Habiba, ta rasu tana da shekaru 79 a duniya.

Sanarwar da Sakataren Masarautar Zazzau, Abdullahi Aliyu Ƙwarbai, ya fitar ta ce za a yi sallar jana’izar surukar sarkin ce bayan Sallar Juma’a a Fadar Sarkin Zazzau.

KU KUMA KARANTA:Ambaliyar ruwa a Zariya ya shafe wani maƙabarta

Jama’a sun shaideta da son zumunci da rikon amana da ibada tukuru kafin rasuwarta

Talakawa ya yawa musamman mata sai kuka suke bisa rashin mamaciyar ta zama mai ɗebe masu kewa a duk lokacin da saka ziyarceta.

Allah yayi mata gafara Amin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here