Allah Ya yi wa shahararren ɗan jarida, Malam Lawal Sa’idu Funtua rasuwa

0
32
Allah Ya yi wa shahararren ɗan jarida, Malam Lawal Sa'idu Funtua rasuwa

Allah Ya yi wa shahararren ɗan jarida, Malam Lawal Sa’idu Funtua rasuwa

Daga Idris Umar Zariya

Allah Ya yi ma shahararen ɗan jaridar nan, Malam Lawal Sa’idu funtua rasuwa. Ya rasu yau alhamis a gidansa na nan Katsina. Za a saka lokaci jana’izarsa.

Lawal saidu ya fara aikinsa na jarida da gidan rediyon jahar Katsina, ya koma jaridar Today, yayi aiki da jaridu da Redio da talabijin daban daban.

Ya kafa kamfanin jaridar shi ta bisa yanar gizo mai suna Blueink. Ya kuma kafa wata ƙungiya ta kare hakkin ‘yan jaridu da marubuta, yana kuma da kamfanin bayar da shawarwari akan harkar sadarwa da hulda da jama’a.

Lawal saidu mai baiwa ne aikin jarida, ya iya rubutu da hausa, turanci da kuma sharhi a rediyo da talabijin.

KU KUMA KARANTA: Allah Ya yi wa ɗan Sarkin Zazzau rasuwa

Lawal yayi sama da shekara goma yana fama da rashin lafiya ya kwanta ya tashi, sai yanzu ciwon ya warke.

Ya rasu ya bar mata , ‘ya’ya da jikoki.
Allah ya jikanshi da Rahama.

Leave a Reply