Alhassan Yahaya ya zama sabon shugaban ƙungiyar ‘yan jarida ta Najeriya

0
21
Alhassan Yahaya ya zama sabon shugaban ƙungiyar 'yan jarida ta Najeriya

Alhassan Yahaya ya zama sabon shugaban ƙungiyar ‘yan jarida ta Najeriya

Daga Ibraheem El-Tafseer

An zaɓi Alhassan Yahaya daga jihar Gombe a matsayin sabon shugaban ƙungiyar ‘yan jarida ta ƙasa (NUJ).

Ya lashe zaɓen ne da ƙuri’u 436, inda ya doke Dele Atunbi, Ma’ajin Ƙasa mai barin gado, wanda ya samu ƙuri’u 97, da Garba Muhammad, wanda ya samu ƙuri’u 39.

Wakilai 602 daga shiyyoyin Najeriya shida har da babban birnin tarayya Abuja, sun hallara a Owerri, babban birnin jihar Imo, domin zaɓen sabon shugaban ƙungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ).

Wa’adin sabon shugaban zai kai shekaru 3 kuma wannan sabon shugaban zai tafiyar da harkokin ƙungiyar cikin waɗannan shekaru 3 ɗin.

Nasarar Yahaya ta zama sabon babi ga NUJ, kuma ana sa ran zai jagoranci ƙungiyar wajen inganta jin daɗin ‘yan jarida da kuma kiyaye ƙa’idojin aikin jarida na gari.

Har zuwa lokacin da Yahaya ya zama shugaban NUJ, shi ne mataimakin shugaban ƙungiyar ta ƙasa (NUJ).

KU KUMA KARANTA: An naɗa sabon darakta a kwalejin kiwon lafiya ta Al-Haroon Zariya

Tun da farko Comrade Christopher Isiguzo, shugaban NUJ mai barin gado na ƙasa, ya ba da tabbacin miƙa mulki cikin kwanciyar hankali, inda ya bayyana cewa ba zai tsoma baki a harkokin tafiyar da sabbin shugabannin ba.

Leave a Reply