Al-Muhajir ya jadadda mahimmancin ilimin taurari a ziyararsa gidan jaridar Neptune Prime

0
295

Fitaccen malamin addinin Musulunci, masanin taurarin gargajiya, kuma fitacce a kafafen sada zumunta na soshiyal midiya, Malam Sharif Al-Muhajiru ya kai ziyarar ban girma a ofishin Neptune Prime’s da ke Abuja ranar Litinin.

Malamin wanda ya samu tarba daga mawallafi kuma wanda ya kafa kamfanin, Dokta Hassan Gimba ya nuna jin daɗinsa kan tarɓar da ya samu daga Neptune Prime.

Da yake jawabi bayan gabatar da jawabin da shugaban ma’aikatansa Saminu Dauda ya yi, malamin ya jaddada muhimmancin likitancin Musulunci, ilmin taurari tare da nuna bakin cikinsa kan yadda fannin ke fuskantar rashin kulawa.

Malamin wanda kuma yake rike da sarautar gargajiya ta Majidadin Yakanaje ya kuma bayyana hanyoyin da zai bi wajen magance matsalar sihiri da aljanu da ke addabar al’ummar mu a yau.

KU KUMA KARANTA:Zamu cigaba da Addu’a ga Yobe da Najeriya don samun zaman Lafiya- Shugaban Izala

Ya ƙara da cewa akwai hanyoyin da za a bi wajen magance matsalar rashin tsaro da rashin shugabanci nagari ta fuskar ruhi.

A nasa ɓangaren, mawallafin jaridar Neptune Prime, Dokta Hassan Gimba ya bayyana jin daɗinsa da ziyarar tare da yin alkawarin duba yadda kamfanin zai yi aiki tare da malamin.

Yayin da yake jaddada mahimmancin ilimi, Dakta Gimba ya ce ya ji daɗin ganin matashi kamar Al-Muhajir da ke ƙoƙarin ƙulla alaƙa tsakanin ilimin taurari da na gargajiya da na zamani, da kuma magungunan ganye.

Leave a Reply