Akwai shari’o’i dubu 39,526 a gaban mu — Kotun Ɗaukaka Ƙara

0
228

Daga Ibraheem El-Tafseer

Shugabar kotun ɗaukaka ƙara, Mai Shari’a Monica Dongban Mensen, ta ce kotun ɗaukaka ƙara na da shari’o’i 39,526 a gabanta.

Mai shari’a Mensen ta bayyana haka a yayin bikin ƙaddamar da sabuwar kalanda shekarar shari’a ta 2023/2024.

Ta ce kotun ɗaukaka ƙara ta samu jimillar ƙararraki dubu 7,295 da kuma ƙararraki 3,665 a shekarar 2022/2023.

“A shekarar shari’a ta 2022/2023, an shigar da jimillar ƙararraki 7,295 da kuma ƙorafe-ƙorafe dubu 3,665 a sassa 20 na kotun.

KU KUMA KARANTA: Ba mu yarda da hukuncin kotu ba, za mu ɗaukaka ƙara har kotun ƙoli – Abba Kabir Yusuf

”Kotu ta kammala ƙararraki dubu 3,765 sannan ta kori ƙararraki 5,617. An kori 1,030 daga cikin waɗannan ƙararraki kuma an ba da izini a kan 10,381.

“Har yanzu kotun tana da jimillar ƙararraki 39,526 da ake sauraro zuwa ranar 31 ga watan Agusta, 2023. Wannan ƙaruwa ce daga dubu 34,037 da ke gaban kotu a shekarar shari’a ta 2021/2022,” in ji ta.

Ta ce an samar da kwamitocin shari’a 98 domin sauraren ƙorafe-ƙorafen zaɓe a faɗin ƙasar nan domin gudanar da jimillar ƙorafe-ƙorafe 1,209 da aka shigar.

Leave a Reply