Akwai Bukatar Yin Gyararraki Kusan 30 Zuwa 40 A Kundin Tsarin Mulkin Najeriya – Hon Auwal Jatau

0
351

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

DAN Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Zaki ta Jihar Bauchi, Honarabul Auwal Mohammed Jatau, ya bayyana cewa da akwai bukatar yin wasu yan gyare-gyare akalla kusan wurare talatin zuwa arba’in a Kudin tsarin mulkin kasar Najeriya wanda dama wasu al’umma masu sukar ke ganin cewa basu dace da tsarin mulkin Demokoradiyya ba.

Honarabul Auwal Jatau, ya bayyana hakan ne a wani zantawarsa da manema labarai inda ya bayyana cewa wannan wani abu ne wanda dama wasu al’umma sun jima suna sukar al’amuran, kana su karan kansu a matsayin wata kwamitin Majalisar Tarayyar sun tabbatar da hakan.

Ya kara da cewa a bisa yunkurin da suka yi domin gano wasu abubuwan da suke da bukatar sauyin, sun fahimci cewa da akwai wasu sassan dake da bukatar sauyin domin mayar da su ta fuskar Demokoradiyya wacce a kan wannan tafarkin ake tafiya a wannan zamanin.

Ya ce “a Kundin Tsarin Mulkin Kasar nan wadda a yau Najeriya ta ke amfani da shi wajen gabatar da tsare-tsare na mulki, an dade ana sukar wasu gabobi daban-daban na wannan kundi da cewa ya kamata ace an canza su, domin masu sukar suna cewa tsari ne wanda Sojoji su ka yi shi domin biyan wasu bukatun kansu a lokacin da suka samu kansu a madafun iko saboda haka bai yi daidai da tsarin mulkin Demokoradiyya da ake tafiya da ita a yau ba.”

“Wadannan abubuwan a kwamitance, mun zauna mun duba abubuwan da wurare daban-daban wanda daga kan abubuwan da suka shafi masu Sarautun Gargajiya da matsayinsu a kasar da kundin tsarin mulki, matsayin harkokin mata da yara, matsayin harkokin Zabe, matsayin mallakar dukiyar data fito daga karkashin kasa kamar ma’adinai irinsu zinari da dai sauran wasu abubuwan masu mahimmanci da ya kamaci ace an sauya musu fasali.”

“Mun zauna, mun aminta da yin wasu yan gyare-gyaren wanda zaman har ya hada da yan Majalisar Dattawa, kana a zaman da muka yi dasu, mun samu fahimtar juna domin samun sauyi a wadannan a kan abubuwan da suke da bukatar sauyi wajen aiwatar da su a matsayin Kundin Tsarin Mulkin a karkashin mulkin Demokoradiyya.”

Da yake tsokaci bisa ziyarar bazata wacce Uwar-gidan shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari ta kaiwa Majalisar, Honarabul Auwal Jatau ya danganta zuwan na ta bisa kudirin ganin cewa an baiwa fannin mata da yara fifiko wanda hakan na daya daga cikin gyare-gyaren da suke da bukatar yi domin samun sauyi a kundin tsarin mulki na kasar.

Acewar mamba na kwamitin gyaran Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, da akwai wasu Kungiyoyi na mata na duniya dana Najeriya wanda suke ganin cewa kason da mata suke samu a hidindimu na Najeriya bai yi musu ba ko ya yi musu kadan, saboda haka a kullum bukatar su shi ne a kara musu wani kaso, wanda a bisa irin wadannan dalilai ne yasa ita Uwar-gidan shugaban Kasa da minista suka kawo musu ziyarar zuwa zauren Majalisar Tarayyar domin wasu biyan bukatunsu na mata da kuma yara.

A karshe, Dan Majalisar Tarayyar mai wakiltar mazabar Zaki ta Jihar Bauchi, Honarabul Auwal Mohammed Jatau, ya bada tabbacin cewa Majalisar Tarayyar na Kokarin ganin cewa an samu wannan sauyin domin sun riga sun gabatar da wannan kudiri a Majalisar, illa lokacin kawai suke jira na ganin cewa an samu tabbacin wadannan abubuwan.

Leave a Reply