Akwai buƙatar samar da sauyin zaman lafiya mai ɗorewa — Maryam Bukar

0
479
Akwai buƙatar samar da sauyin zaman lafiya mai ɗorewa — Maryam Bukar

Akwai buƙatar samar da sauyin zaman lafiya mai ɗorewa — Maryam Bukar

Sabuwar mai bada shawara kan harkokin lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Maryam Bukar-Hassan (Alhan_islam) ta bayyana cewa samar da dauwamammen zaman lafiya a duniya shi ne burinsu.

Maryam ta bayyana hakan ne a lokacin da babban jami’in kula da ayyukan jin ƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya, Mohammed Malick Fall, ke maraba da ita a ofishin majalisar da ke Abuja.

Mohammed ya jaddada muhimmancin samar da zaman lafiya, yana mai cewa zaman lafiya wani abu ne da ake buƙata don jin daɗin rayuwar ɗan Adam, kuma idan ba a same shi ba, ci gaban dimokuraɗiyya da kuma ’yancin ɗan Adam ba zai samu ba.

Ya bayyana damuwarsa kan yadda aka sake samun ɓullar tashe-tashen hankula a Nijeriya da ma duniya baki ɗaya, yana mai cewa hakan koma baya ne ga ci gaban da aka samu tun kafuwar MƊD shekara 80 da suka gabata.

Da take nata jawabin Maryam Bukar Hassan ta ce, akwai buƙatar a samar da wani shiri na kawo sauyi wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

KU KUMA KARANTA: MƊD ta ƙaddamar da bugu biyu na ‘Muryoyin Sahel’

Har ila yau, Mohammed Fall ya yaba da yadda aka naɗa Maryam Bukar-Hassan a matsayin, ya ce hakan yazo a daidai lokacin da ya dace kuma mai mahimmanci, yana mai bayyana irin ƙarfin gwiwar da yake da shi akanta na za ta sauke nauyin da aka ɗora mata, mussaman wajen isa ga al’umma da matasa ta hanyoyin diflomasiya.

Yana mai cewa, “Ku ne muryar matasa, muryar jagorancin mata,” in ji shi. Ya kuma jaddada irin rawar da taka wajen tsara makomar neman zaman lafiya.

Ya kuma bayyana cewa, nauyin da ke kanta ya yi fice a Nijeriya har zuwa ayyukan da duniya ke yi. Duk da irin rawar da take takawa a duniya, Fall ya ba ta tabbacin goyon bayan Majalisar Ɗinkin Duniya.

Hakazalika Maryam Bukar-Hassan ya jaddada cewa, idan har ba zaman lafiya ba, yadda za a iya cimma muradun ci gaba mai ɗorewa (SDGs) kuma zai kasance mara amfani.

“Ba maganar talauci idan zaman lafiya da yin adalci sun tabbata,” in ji ta,

Ta kuma ƙara da cewar, tabbatar da yunƙurin zaman lafiya ta hanyar haɗa harsunan asalin ƙabilu da al’adu na gargajiya ne fatanmu dole mu haɗa da harshen Ingilishi,” in ji ta.

Idan har muna son mu kai ga cimma nasara dole ne, mu komo hanyar yadda da al’ummominmu suka tsara. Wannan hanya na nufin tabbatar da gina zaman lafiya mai ɗorewa, musamman a yankunan da asalin al’adu ke taka muhimmiyar rawa a cikin zamantakewa.

Leave a Reply