Ofishin Hukumar Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da ke Minna ya sake sanar da wasu mazauna jihar Kwara kan wata ambaliyar ruwa da ke tafe.
Zainab Saidu, shugabar ofishin hukumar NEMA a Minna, ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa ana sa ran wannan ambaliya musamman a ƙananan hukumomin Ilorin ta Yamma da Ilorin ta Gabas na jihar.
Ta ce ana sa ran ƙananan hukumomin biyu za su fuskanci ambaliyar ruwa a cikin watannin Yuli da Nuwamba.
Misis Saidu ta ce hasashen yana ƙunshe ne a cikin hasashen ambaliyar ruwa na shekara-shekara da Hukumar Kula da Ruwa ta Najeriya, NIHSA, ta fitar a farkon shekarar.
“A cikin wannan hasashen, ƙananan hukumomin Ilorin ta Yamma da Ilorin ta Gabas an karkasa su ne a cikin yankunan da ake ƙira ‘Babban Hatsarin Ambaliyar Ruwa’ waɗanda ake hasashen za su fuskanci ambaliya daga watan Yuli zuwa ƙarshen shekara.
KU KUMA KARANTA: Uwargidan shugaban ƙasa ta bayar da tallafin kuɗi ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Abuja
“Sauran ƙananan hukumomin kamar Patigi, Offa, Edu da Oyun, duk da ana ƙiransu da matsakaitan haɗarin ambaliya, suna iya fuskantar ambaliyar ruwa daga Yuli zuwa Nuwamba.
“Yana da kyau a lura cewa Kwara ta fara fuskantar ambaliyar ruwa da iska a wasu daga cikin waɗannan yankuna, don haka akwai buƙatar jama’a su yi taka-tsan-tsan don gujewa sake ɓarnatar dukiyoyi da asarar rayuka,” inji ta.
Madam Saidu ta buƙaci mazauna jihar a duk wuraren da aka gano su tabbatar da tsaftace magudanan ruwa domin gujewa toshewar hanyoyin ruwa.
“Waɗanda ke zaune a filayen ambaliya da bakin kogi dole ne a cikin gaggawa su shirya don ƙaura zuwa wurare mafi aminci da tsaro.
“Hakan ya faru ne saboda akwai alama mai ƙarfi da ke nuna cewa ruwan da ke gefen kogin Neja yana ƙaruwa kuma hakan zai ƙara ƙarfin magudanan ruwa.
“Saboda haka hakan zai haifar da ambaliya a bakin kogin kuma hakan zai yi tasiri sosai ga mazauna kewayen kogunan,” in ji ta.
Jami’in hukumar ta NEMA ya ƙara da cewa rigakafi ita ce hanya mafi inganci na maganin bala’o’i a duniya.
“Don haka dole ne jama’a su ɗauki nauyin bin waɗannan gargaɗin don ceton rayukansu da dukiyoyinsu.”
[…] KU KUMA KARANTA: Akwai barazanar ambaliyar ruwa a jihar Kwara – NEMA […]
[…] KU KUMA KARANTA: Akwai barazanar ambaliyar ruwa a jihar Kwara – NEMA […]
[…] KU KUMA KARANTA: Akwai barazanar ambaliyar ruwa a jihar Kwara – NEMA […]