Aikin ƙidayar 2023 zai lashe naira biliyan 400

Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa, (NPC) ta ce an ware sama da Naira biliyan 400 domin ƙidayar jama’a ta shekarar 2023.

Jick Lawrence, shugaban sashen hulɗa da jama’a na NPC a Filato, shi ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke gabatar da maƙala a wajen wani taron ƙarawa juna sani na yini ɗaya ga ‘yan jarida kan yadda za a samar da ingantaccen rahoto kan ƙidayar jama’a, a Jos a ranar Litinin.

Lawrence ya ce kawo yanzu an kashe kimanin Naira biliyan 100 a shirye-shiryen tunkarar wannan aiki na ƙidaya da za a yi shi nan gaba kaɗan.

“Sama da Naira biliyan 400 aka ware don kashewa a ƙidayar wannan shekara ta 2023.

“Kawo yanzu an kashe kimanin Naira biliyan 100 kan shirye-shiryen tunkarar wannan aiki na ƙidayar jama’a babban aiki ne mai matuƙar tasiri,” in ji shi.

KU KUMA KARANTA: UNICEF na shirin yiwa yara miliyan ɗaya rejista a Bauchi

Lawrence, wanda ya jaddada cewa ƙidayar ta samu riba mai yawa a fannin zamantakewa da tattalin arziƙi, ya bayyana cewa wasu daga cikin kuɗaɗen za su shiga cikin bunƙasa rayuwar ‘yan Najeriya kusan miliyan 1.5 ne.

Ya ce waɗanda aka ɗauka aikin, za a biya su kuɗaɗe daga N100,000 zuwa 150,000 ga kowane mutum.

Ya ƙara da cewa za a ɗauki hayar motoci 56,000 don inganta zirga-zirgar ma’aikata da kayan aiki, sannan kuma za a sayo kayan aiki zamani na kusan 800,000 Personal Digital Assistant (PDAs).


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *