Ademola Lookman na kan gaba wajen lashe kyautar gwarzon ƙwallon ƙafa na Afrika ta bana

0
28
Ademola Lookman na kan gaba wajen lashe kyautar gwarzon ƙwallon ƙafa na Afrika ta bana
Ademola Lookman

Ademola Lookman na kan gaba wajen lashe kyautar gwarzon ƙwallon ƙafa na Afrika ta bana

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afrika CAF, ta fitar da jerin sunayen ‘yan wasa biyar da suka fi cancanta domin lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Afrika na shekarar 2024 a hukumance, inda ɗan wasan Super Eagles ta Najeriya, Ademola Lookman ya jagoranci jerin sunayen.

A wannan jadawali da hukumar ta CAF ta fitar, kyaftin ɗin Najeriya Wiliam Trost Ekong bai samu damar zama daga cikin sunayen yan wasan biyar ba.

Ɗan kasar Cote d’Ivoire, Simon Adingra; Serhou Guirassy na Guinea; Ɗan wasan baya na Morocco, Achraf Hakimi, da mai tsaron gida na Afrika ta Kudu, Ronwen Williams, su ne sauran ‘yan wasa huɗu da aka zaɓa don lashe kyautar gwarzon ɗan wasan CAF na bana.

Sauran nau’o’in kyaututtukan da aka sanar a ranar Litinin sun hada da Gwarzon Golan Shekara, Gwarzon Dan Wasan Kwallon Kafa na Interclub, Koci Na Shekara, Gwarzon Ɗan Wasa Na Shekara, Gwarzuwar Ƙungiya da kuma gwarzuwar tawagar ƙwallon ƙafar ƙasa na Shekara.

KU KUMA KARANTA: Ƙwallon ƙafa: Najeriya ta koma na 36 a taka leda a duniya

 Bikin mai kayatarwa akan tsara shi domin nuna irin cigaba da harkar kwallon kafa a Afrika ta samu da kuma karrama yan wasa da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da sukafi taka rawa a shekarar da ta gabata,wanda zai kai ga lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Afirka na CAF na bana a ɓangaren maza da mata.

Leave a Reply