Adadin waɗanda suka mutu a Gaza ya zarta wanda hukumomi suka bayar – Bincike
Binciken ya yi ƙiyasin cewa tsakanin watan Oktoban 2023 zuwa Yunin 2024, an sami mutuwar Falasdinawa sama da 64,000 sakamakon tashin hankali a Gaza, wanda ke nuni da cewa ma’aikatar lafiya ta Hamas da ke yankin, ta rage a rahoton adadin da ta bayar na wadanda suka mutu da kusan kashi 41%.
Adadin wadanda suka mutu a yakin da Isra’ila ta ke yi da mayakan Hamas a Gaza ya zarta adadin da ake bayyanawa a hukumance, a cewar wata kididdigar masu bincike a makarantar kula da tsaftar muhalli da magunguna ta London, da aka wallafa a ranar Alhamis a mujallar lafiya ta Lancet.
KU KUMA KARANTA:Paparoma Francis ya yi Alla-wadai da matakan Sojin Isra’ila a Gaza
Binciken ya yi kiyasin cewa tsakanin watan Oktoban shekara ta 2023 zuwa Yunin shekara ta 2024, an sami mutuwar Falasdinawa sama da 64,000 sakamakon tashin hankali a Gaza, wanda ke nuni da cewa ma’aikatar lafiya ta Hamas da ke yankin, ta rage a rahoton adadin da ta bayar na wadanda suka mutu da kusan kashi 41%.
Adadin hukuma na waccan lokacin shine mutane 37,877 suka mutu.
Kusan kashi 59 cikin 100 na wadanda suka mutu mata ne, ko yara ko kuma tsofaffi, a cewar rahoton wanda ya yi daidai da wasu alkaluma na daban. Binciken bai bayyana adadin mayakan Hamas da suka mutu ba.
Wata kididdiga ta daban ta Majalisar Dinkin Duniya ta sama da mutane 8,000 da aka tabbatar sun mutu tsakanin watan Nuwamban shekara ta 2023 zuwa Afrilun shekarar 2024, ta bayyana cewa kashi 44% na wadanda abin ya shafa kananan yara ne, yayin da kuma 26% ne mata.