Wani abun fashewa a Yobe ya tashi a fitacciyar kasuwar dabbobi

0
88
abun fashewa a Yobe ya tashi a fitacciyar kasuwar dabbobi

Wani abun fashewa a Yobe ya tashi a fitacciyar kasuwar dabbobi

Wani abun fashewa da ake zargin bam ɗin da aka birne ne ya tarwatse a fitacciyar kasuwar dabbobin nan ta Buni Yadi dake ƙaramar hukumar Gujba ta jihar Yobe.

Wani mazaunin garin Buni Yadin, Ali Hassan ya shaidawa tashar talabijin ta Channels ta wayar tarho cewar, al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12 da rabi na ranar Juma’a, kuma ya raunata wata yarinya.

Shima kakakin shiya ta 2 na aikin wanzar da zaman lafiya na hadin gwiwa mai taken “Operation Hadin Kai”, Kyaftin Muhammad Shehu ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce sojoji sun yi nasarar gano wani bam din da aka birne a kasuwar tare da tarwatsa shi.

KU KUMA KARANTA:An kama ɓarayin da ke haurawa gidajen mutane suna sata a Yobe

Ya ƙara da cewa mutum guda da fashewar ta shafa, na samun kulawa a ɗaya daga cikin asibitocin da ke garin Buni Yadi.

Ya kuma jaddada cewa al’amarin ba harin ƙunar bakin wake bane illa kawai bam ne da aka birne a ƙasa.

Garin Buni Yadi mai tazarar kilomita 54 tsakaninsa da Damaturu babban birnin jihar, na cikin karamar hukuma a jihar da ta fi fama da ayyukan ta’addanci, inda ta kasance ƙarƙashin mayaƙan Boko Haram tsawon shekaru 2.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here