Abin da ya sa Gwamnan Kano ya kori hadimansa guda 2
Daga Jameel Lawan Yakasai
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kori wasu manyan mataimaka na musamman guda biyu bayan samun hujjar laifinsu daga kwamitocin bincike, tare da wanke wani hadimi daga zargi.
Wadanda aka kora su ne Abubakar Umar Sharada, SSA kan Shirya Taron Siyasa, bisa tabbatar da hannunsa wajen bayar da belin wani babban dillalin miyagun ƙwayoyi, da kuma Tasiu Adamu Al’amin Roba, SSA a Ofishin Sakataren Gwamnati, wanda aka kama da laifin sake buhunan hatsi na tallafi a Sharada a 2024.
Dukkaninsu an umarce su da su mika dukiyar gwamnati kafin 11 ga Agusta 2025, tare da gargadin kada su ƙara bayyana kansu a matsayin jami’an gwamnati.
KU KUMA KARANTA: Kwamishinan Sufuri na Kano ya karɓi cin hancin Dala Dubu 30 kan karɓar belin dillalin miyagun ƙwayoyi
A gefe guda, gwamnatin jihar ta wanke Hon. Musa Ado Tsamiya, mai bada shawara na musamman kan magudanan Ruwa, bayan kwamitin bincike ya tabbatar da cewa bai aikata laifin da ake zarginsa ba.
Gwamna Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatinsa na tsaurara doka, gaskiya, da rashin sassauci ga rashawa, yana gargadin jami’an gwamnati da su kiyaye amana da ɗabi’a mai kyau a aiki da rayuwarsu ta yau da kullum.









