A tabbata an bi haƙƙin waɗanda aka kashe a Edo, an kuma biya su diyya – Gwamnan Kano

0
160

A tabbata an bi haƙƙin waɗanda aka kashe a Edo, an kuma biya su diyya – Gwamnan Kano

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga gwamnatin jihar Edo da ta tabbatar ta bi hakkin mafarauta 16 da wasu ɓatagari su ka ƙone har lahira, tare da baiwa iyalan su diyyar rayukan da aka salwantar.

Da ya ke jawabi yayin da gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya kawo ziyarar ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar Kano a yau Litinin a gidan gwamnati, Yusuf ya yi kira ga gwamnan da ya tabbata an bi hakkin waɗanda aka kashe ta hanyar hukunta waɗanda su ka aikata ta’asar.

Ya kuma yi kira ga gwamnan da ya cika alkawarin da ya ɗauka na biyan diyyar rayuka 16 da aka hallaka ga iyalan su.

KU KUMA KARANTA:Gwamnan Edo ya ziyarci Kano don jajantawa kisan mafarauta 16

“Ina da yaƙinin gwamna Okpebholo mutum ne mai magana ɗaya. Na san zai cika alkawarin da ya ɗauka na biyan diyya da kuma yin adalci ga iyalan waɗanda aka kashe,”

Gwamna Yusuf ya kuma yi kira ga hukumomi da su tabbata sun baiyana fuskoki da sunayen wadanda aka kama da zargin kisan.

A nasa jawabin, Gwamna Okpebholo ya ce shi an taba riƙe shi a Kano a hannun wani dan kasuwa bahaushe, saboda haka ba zai bari a cuci hausawa ba.

Ya jaddada aniyar gwamnatin sa na ganin an bi hakkin waɗanda aka kashe da kuma biya su diyya.

Okpebholo ya nuna kaduwar sa da kisan, inda aya baiyana cewa ya samu labarin da misalin ƙarfe 4 na asuba, inda ya kara da cewa yana jin labarin ya garzaya wajen da kuma daukar matakan da suka dace.

Leave a Reply