A Azare, ƙungiyoyi sun yi ƙira ga mahukunta da su dakatar da hawa Dawakai a lokacin bukukuwa

0
34
A Azare, ƙungiyoyi sun yi ƙira ga mahukunta da su dakatar da hawa Dawakai a lokacin bukukuwa

A Azare, ƙungiyoyi sun yi ƙira ga mahukunta da su dakatar da hawa Dawakai a lokacin bukukuwa

Daga Ibraheem El-Tafseer

Wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adama mai suna ‘Muryar Talaka Awareness initiative’ reshen jihar Bauchi, tare da ƙungiyar ‘Justice and Youth Awareness Forum’ (JUYAF) Bauchi, sun nuna ɓacin ransu bisa yadda mahaya Dawakai a garin Azare ke ci gaba da kashe mutanen a yayin wasanin guje-guje da suke yi duk lokacin da suka fito dan shagulgulan buki.

Ƙungiyoyin sun ce kusan duk lokacin da ake bukukuwa mahaya Dawakan sukan ta guje guje goshin Magariba wanda hakan yakan sa su buge mutane, har ya kai ga an rasa rayuka.

Wannan ƙiran ya fito ne daga bakin sakataren Ƙungiyar Ahamad Arab a yayin da yake zantawa da manema labarai a garin Azare ta jihar Bauchi.

Ya ce, wannann abin takaici ne a ce mahaya Dawakai suna guje – guje a cikin gari kuma daidai lokacin da duhu ya shigo, ya ce wannan ya saɓawa duk wata doka.

KU KUMA KARANTA: Kwankwaso ya caccaki ;yansanda kan yunƙurin hana mauludin Tijjaniyya a Kano

Kuma wannan abin ya sha faruwa ba sau ɗaya ba, a garin na Azare ko a makon nan, hakan ya faru sakamakon yadda wani mahayin Doki ya buge wani bawan Allah Mai suna, Yusuf Adamu wanda buge shi ɗin ya jawo sanadin rasuwarsa nan take.

Dan haka waɗannan ƙungiyoyin sun jima suna binciken da kuma tara alƙalumman yawan mutanen da aka rasa rayukansu sakamakon buge mutane da mahaya Dokin suke yi a yayin bukukuwa.

Wannan ƙungiya na ƙira da masu ruwa da tsaki da su shigo ciki domin neman mafita domin kare rayuwan al’ummar garin Azare. Domin akwai dokoki na musamman na ƙasa da na ‘yancin ɗan Adam da suka haramta irin wannan gangancin a cikin mutane.

A ƙarshe ya yi ƙira da a tanadar wa waɗannan mahaya wajan da za su nayin wasanin bukukuwa ba tare da sun shigo unguwanin cikin gari suna guje-guje ba.

Leave a Reply