Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

0
0

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Rundunar soji ta kama ’yansanda huɗu bisa zargin ci gaba da rakiya ba tare da izini ba ga manyan mutane, lamarin da ya saɓa wa umarnin shugaban ƙasa na janye ’yan sanda daga gadin manyan mutane.

Majiyoyin ’yansanda sun shaida wa Zagazola Makama cewa an kama jami’an ne a ranar 17 ga Disamba da misalin ƙarfe 9:30 na safe, yayin da ake zargin suna bakin aikin rakiyar wani babban mutum.

KU KUMA KARANTA: Sojoji sun ceto mutune 7 da aka yi garkuwa da su a Kano 

A cewar majiyoyin tsaro, jami’an soji ne suka kama ’yansandan bayan sun karya umarnin shugaban ƙasa na janye jami’an ’yan sanda daga rakiyar manyan mutane.

Majiyoyin sun ƙara da cewa ’yansandan sun sanya kayan aiki (uniform) masu kama da na Hukumar tsaron farar hula ta kasa (NSCDC), wai domin gujewa ganowa da yaudarar jami’an da ke sa ido kan aiwatar da dokar.

Tun daga lokacin da aka kama su, an tsare jami’an, sannan aka fara matakan ladabtarwa a kansu bisa tanadin ƙa’idojin da ke aiki.

Leave a Reply