A daina biyan kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane – Christopher Musa

0
66
A daina biyan kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane - Christopher Musa

A daina biyan kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane – Christopher Musa

Majalisar Dattawa ta tabbatar da tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, a matsayin sabon Ministan Tsaro na Najeriya.

Tabbatarwar ta biyo bayan tantancewa inda ‘yan majalisa suka yi masa tambayoyi kan matsalolin tsaro da tarihin aikinsa.

Musa ya yi alƙawarin aiki tare da dukkan hukumomin tsaro da jama’a don magance kalubalen tsaro.

Jaridar TheCable ta rawaito cewa, Musa ya yi kira da a daina biyan kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane da masu tayar da kayar baya, yana mai cewa hakan na ƙara musu ƙarfin makamai.

KU KUMA Tinubu ya nemi majalisa ta amince ya naɗa Janar Christopher Musa a matsayin sabon Ministan Tsaro

Ya kuma bukaci samar da kundin bayanai na ƙasa guda ɗaya, da kuma ƙarin tasiri daga jihohi da ƙananan hukumomi wajen yaki da rashin tsaro.

Musa ya ce kisan-kisan da ake yi a ƙasar ya shafi kowa ba tare da bambanci ba.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yaba da irin amsoshin da Musa ya bayar, sannan ‘yan majalisa suka amince da nadinsa ta hanyar kuri’ar murya.

Leave a Reply