Gwamnan Bauchi ya dakatar da kwamishinar harkokin mata
Daga Idris Umar Zariya
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya sallami Hajiya Zainab Baban Takko daga kan muƙaminta na Kwamishinar kula da harkokin mata da bunƙasa ci gaban yara ƙanana.
Matakin na ɗauke ne cikin wata sanarwar da babban mashawarcin gwamnan kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Mukhtar Gidado, ya fitar a jiya, inda ya tabbatar da cewar sallamar ta fara aiki nan take ba tare da ɓata wani lokaci ba.
Gidado ya bayyana matakin a matsayin wani ɗan ƙaramin garambawul ga majalisar zartarwa ta jihar.
KU KUMA KARANTA: Gwamnan Bauchi ya naɗa ɗan ƙasar China a matsayin mai bashi shawara kan tattalin arziƙi
Babu wani dalilin da aka bayar na korar Kwamishinar, sai dai gwamnan ya gode mata bisa gudunmawar da ta bayar tare da mata fatan alkairi a rayuwarta na gaba.
Wata majiya ta labarta cewa gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya rantsar da Hajiya Zainab Baban Takko a matsayin Kwamishina ne a ranar 9 ga watan Satumban 2024 tare da wasu sabbin kwamishinoni biyu.
Kafin ta hau kan wannan kujerar, ta zama shugaban riƙon ƙwarya na ƙaramar hukumar Bauchi wanda gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya naɗata a watan Yulin 2023.









