KMT ya sake gyara Gadar da ya gina a Rugar Fulani Potiskum (Hotuna)

0
168
KMT ya sake gyara Gadar da ya gina a Rugar Fulani Potiskum (Hotuna)
Alhaji Kashim Musa Tumsa MFR (KMT)

KMT ya sake gyara Gadar da ya gina a Rugar Fulani Potiskum (Hotuna)

Idan ba a manta ba, a watannin da suka gabata, Alhaji Kashim Musa Tumsa MFR ya gina Gada a Rugar Fulani da ke Potiskum jihar Yobe.

Biyo bayan ruwan sama da aka yi kamar da bakin ƙwarya a Potiskum, wanda hakan har ya jawo ambaliyar ruwan, haɗe da rushewar gidajen jama’a da dama, to hakan ya sa ita ma Gadar gefenta ya zaizaye, amma Gadar tana tsaye ƙyam. Hakan yana nuna cewa Gadar an yi mata ingantaccen aiki.

KU KUMA KARANTA: An ƙaddamar da buɗe gadar da KMT ya gina a Rugar Fulani Potiskum (Hotuna)

Duk lokacin da aka yi aiki irin wannan, to bayan buɗe ta (commissioning), an damƙa ta a hanun al’ummar unguwar, to alhakin kula da Gadar da gyara ta, yana hanun al’ummar unguwar. Amma KMT bai yi ƙasa a gwiwa ba, ya sake komawa ya gyara musu inda gefen Gadar ya zaizaye.

An yiwa Gadar gini mai ƙarfi a ɓangare 4 na gefen Gadar, don ƙara inganta ta, da hana zaizayewa nan gaba.
Jama’ar unguwar suna ta yi masa addu’ar fatan alheri da fatan samun nasara a dukkan abin da ya sa a gaba.

Leave a Reply