A cikin mako 2, jami’an tsaron Najeriya 53 ne suka rasa ransu 

0
136
A cikin mako 2, jami'an tsaron Najeriya 53 ne suka rasa ransu 

A cikin mako 2, jami’an tsaron Najeriya 53 ne suka rasa ransu

Daga Jameel Lawan Yakasai

Aƙalla jami’an tsaro 53 ciki har da sojoji, ƴan sanda, jami’an NSCDC, kwastam, da na shige da fice da ƴan sa kai, aka kashe a sassa daban daban na Najeriya cikin makonni biyu da suka gabata.

Yawancinsu ƴan bindiga ne suka halaka su yayin hare hare, wasu kuma a wuraren binciken tsaro.

Rahotanni sun nuna cewa daga Janairun 2023 zuwa Oktoban 2024 an kashe jami’an ’yan sanda 229 a faɗin ƙasar.

Masu kisan sun haɗa da ƴan bindiga, Boko Haram, IPOB, da ƴan fashi da kuma ƙungiyoyin asiri.

KU KUMA KARANTA: Jami’an tsaro sun kama wata matashiya da ke kai wa ‘Bello Turji’ makamai

Sabbin hare haren sun fi kamari a jihohin Benue da Kogi, inda aka kashe jami’an tsaro da dama tare da sace wasu.

Sai dai hukumar DSS ta gurfanar da mutane tara a Abuja kan zargin kisan gilla, fataucin makamai da kai hare hare a Benue da Filato.

Leave a Reply