Sowore da Ɗan Bello sun jagoranci jami’an ‘yansanda da suka yi ritaya zanga-zanga, duk da gargaɗin da aka yi musu

0
367
Sowore da Ɗan Bello sun jagoranci jami'an 'yansanda da suka yi ritaya zanga-zanga, duk da gargaɗin da aka yi musu
Sowore da Ɗan Bello

Sowore da Ɗan Bello sun jagoranci jami’an ‘yansanda da suka yi ritaya zanga-zanga, duk da gargaɗin da aka yi musu

Ɗan takarar shugaban ƙasa na African Action Congress (AAC), a zab6en 2023, Omoyele Sowore da Ɗan Bello da wasu masu fafutuka sun jagoranci jami’an ‘yansanda da suka yi ritaya gudanar da zanga-zanga a birnin Abuja.

An bayyana cewa zanga-zangar na da nufin neman a kyautata jin daɗin jami’an rundunar ‘yansandan Najeriya.

Ƙungiyar ‘yansandan Najeriya da suka yi ritaya sun sha alwashin za su yi zanga-zanga a harabar majalisar dokokin ƙasar daga nan kuma su wuce hedikwatar rundunar, inda duka yi ƙira da a cire su nan take daga shirin bayar da gudunmawar fansho.

KU KUMA KARANTA: Rundunar ‘yansanda ta ƙasa ta janye gayyatar da ta yi wa Sarkin Kano Sanusi II

Sun bayyana shirin fensho a matsayin “wariya”, inda suka bayyana cewa mambobinsu suna ta mutuwa.

Kwamitin hulɗa da jama’a na ‘yan sanda, PCRC, ya yi gargaɗi game da zanga-zangar, inda ya yi ƙira ga waɗanda suka yi ritaya da su koma kan teburin tattaunawa.

A cewar PCRC, zanga-zangar wani yunƙuri ne na ɓata sunan Sufeto Janar na ‘yansanda, IGP da kuma gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

Leave a Reply