Ɗaurarru 62 sun kammala karatun sakandire a gidajen gyaran hali na Kano

0
256
Ɗaurarru 62 sun kammala karatun sakandire a gidajen gyaran hali na Kano

Ɗaurarru 62 sun kammala karatun sakandire a gidajen gyaran hali na Kano

Daga Shafaatu Dauda Kano

Hukumar dake kula da gidajen gyaran hali na jihar Kano, ta gudanar da taron yaye dalibai 62 wadanda suka kammala karatun Sakandire daga cikin daurarrun dake zaune a gidajen gyaran halin jihar.

 

Kakakin hukumar, CSC Musbahu Lawan Kofar Nassarawa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya aiko wa jaridar Neptune prime Hausa, inda ya ce tuni daliban sun gudanar da jarrabawar NECO da kuma NBAIS.
A cewar sanarwar, “Wannan ilimi zai taimaka musu wajen sauya rayuwar su zuwa mutanen kirki da zarar an sallame su daga gidan, ta yadda zasu koma cikin al’umma kuma su amfani kansu dama mutane gaba-daya”.

KU KUMA KARANTA:KNUPDA ta rushe gine-ginen da akayi ba bisa ƙa’ida ba a Kano

Kuma wannan yana cikin tanadin sabuwar dokar hukumar ta 2029, wadda ta zamanantar da aikin hukumar ta hanyar samar da tsarin koyon karatu da sana’oin dogaro da kai ga mazauna gidan.
Harma a jawabinsa Kwantirolan hukumar na jihar Kano, Ado Inuwa, ya godewa babban Kwantirolan hukumar na Najeriya, CGC Sylvester Ndidi Nwakuche, a bisa cikakken goyon bayan da yake bawa reshen hukumar na Kano ta fuskar walwalar mazauna gidan da kuma kayan koyon karatu da sana’oin dogaro da kai.
Bugu da kari ya kuma godewa Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusif, a bisa gudunmawar da ya bayar ga ilimin mazauna gidan, wanda hakan ne ya basu damar cin jarrabawar tasu musamman ta darasin turanci da lissafi, inda ya hore su da zama jakadu na gari kamar yadda yake cikin shirin shugaban kasa Bola Tinubu na sabunta fata wato “Renewed Hope Agenda”.
A nasa jawabin gwamnan Kano, wanda ya sami wakilcin Sakataren gwamnatin Jihar, Umar Ibrahim Faruk, ya bayyana cewa gwamnati ta yi matukar farin ciki da samun wannan nasara ta maida daurarru zuwa masu ilimin boko, a inda ya ce gwamnatinsu ta himmatu wajen bawa harkar ilimin daurarrun fifiko domin amfanin rayuwar su.

Leave a Reply