Mummunar gobara a Kano ta jikkata yaro, ta janyo asarar dukiya mai yawa

0
403
Mummunar gobara a Kano ta jikkata yaro, ta janyo asarar dukiya mai yawa

Mummunar gobara a Kano ta jikkata yaro, ta janyo asarar dukiya mai yawa

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Tashin gobara ya ƙone wani bene mai hawa biyu a yankin Aba by Court Road dake ƙaramar hukumar Fagge ta jihar Kano, yayi sanadiyar jikkatar yaro ɗaya da asarar dukiyar miliyoyin kuɗi.

Lamarin ya faru a safiyar Talata, wanda wutar ta fara ci a wani bangaren ginin da wata uwa ta bar ɗanta mai kimanin shekaru 3, kuma wutar ta illata shi kafin a kai ga ceto shi.

Zuwa yanzu ƙaramin yaron na cigaba da karɓar magani, bayan samun nasarar ceto rayuwar sa.

KU KUMA KARANTA:Gobara ta tashi a gidan mai sakamakon fashewar tanka a Neja

An bayar da rahoton cewa jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Kano sun yi hanzarin kai ɗauki tare da shawo kan gobarar akan lokaci

Kwamishinan yan sandan Kano CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ziyarci wajen da aka samu tashin gobarar, inda ya jajanta tashin gobara da kuma bayar da umurnin gudanar da bincike don gano musabbabin wutar. Ya kuma yi kira ga al’umma su riƙa kiyaye aikata abubuwan da ka’iya haddasa tashin gobara.

Leave a Reply