Jami’an tsaron Somaliya sun yi nasarar kashe mayaƙan Al-Shabab da suka kai hari wani Otel

0
21
Jami'an tsaron Somaliya sun yi nasarar kashe mayaƙan Al-Shabab da suka kai hari wani Otel

Jami’an tsaron Somaliya sun yi nasarar kashe mayaƙan Al-Shabab da suka kai hari wani Otel

An fara kai harin ne a ranar Talatar da ta gabata, inda wata mota shake da bama-bamai ta tarwatse a Otel din Alkhahira, wanda ya ke mazaunin dattijan gargajiya da jami’an soji da ke da ruwa da tsaki wajen hada kai da gwamnatin kasar a yakin da ake yi da al-Shabab.

Magajin garin Beledweyne, Omar Alasow, a ranar Laraba ya ce jami’an tsaro “sun yi nasarar kawo karshen harin” kuma mayakan al-Shabab shida sun mutu. Amma har yanzu dai ba a san adadin fararen hula da aka kashe a harin ba.

KU KUMA KARANTA:Ƙasar Masar za ta aika da dakarunta aikin wanzar da zaman lafiya a Somalia

Kungiyar al-Shabab mai alaka da al-Qaida ta dauki alhakin kai harin.

Baledweyne mai tazarar kilomita 335 (kilomita 208) arewa da Mogadishu babban birnin kasar, shi ne babban birnin yankin Hiran, kuma wuri mai muhimmanci a yakin da ake yi da kungiyar ta al-Shabab.

Kiyasin adadin wadanda suka mutu sakamakon harin ya banbanta. Wani mazaunin yankin mai suna Muhsin Abdullahi ya ce an kashe mutane shida da suka hada da wasu fitattun dattawan gargajiya biyu. Sai dai wani shaida, Hussein Jeelle Raage, ya ce uku daga cikin iyalansa na cikin akalla mutane 11 da ya san sun mutu.

Leave a Reply