An kawo sabon Kwamishinan ‘yansanda a Kano
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Hukumar kula da ayyukan ‘yansanda ta kasa, ta amince da nada Dr, Ibrahim Adamu Bakori, a matsayin sabon kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano.
KU KUMA KARANTA:Tinubu ya sauya sunan Jami’ar Ilimi ta Kano zuwa sunan Yusuf Maitama Sule
Bakori dan asalin jihar Katsina, ya maye gurbin tsohon kwamishinan ‘yan sanda Salman Dogo Garba, wanda aka kara masa girma zuwa mukamin mataimakin sufeto Janar na ‘yan sanda.