Hukumar Hisbah a Kano ta haramta wasan tashe a faɗin Jihar
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da haramta kidan Gwauro, da ake fara gudanarwa a ranar 10 ga watan Azumin Ramadan.
KU KUMA KARANTA:‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wani matashi a Jihar Kano
Mataimakin kwamandan hukumar Sheikh Mujahideen Aminudden ne ya bayyana hakan, inda ya ce kiɗan gwauro ya asali ya samo daga masu bautar tsumburbura, sannan musulunci bai yadda da hakan ba.