‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane a garin Zakirai da ke Kano

0
13
'Yan bindiga sun yi awon gaba da wani matashi a Jihar Kano

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane a garin Zakirai da ke Kano

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Yan bindiga sun kai hari tare da sace wani matashi a garin Zakirai dake karamar hukumar Gabasawa a nan Kano.

Yayin wannan hari yan bindigar sun yi garkuwa da wani matashi Mohammed Bello, ɗan shekara 20, sannan wani mai suna Abubakar ya ji rauni.

KU KUMA KARANTA:Gwamnan Kano ya bawa ƙungiyar ‘yan jaridu buhunan shinkafa 450

Rahotanni sun tabbatar da cewa mutanen sun kai hari gidan wani mutun mai suna Alhaji Yusha’u Ma’aruf, wanda ma’aikaci ne a wani asibiti mai zaman kansa a garin na Zakirai.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’an ƴan sanda sun fara neman maharan, Kuma kokarin ceto wanda suka yi garkuwa da shi.

Leave a Reply