Gamayyar gwamnonin arewa sun yi alhinin rasuwar Sheikh Sa’eed Hassan Jingir

0
45
Gamayyar gwamnonin arewa sun yi alhinin rasuwar Sheikh Sa'eed Hassan Jingir

Gamayyar gwamnonin arewa sun yi alhinin rasuwar Sheikh Sa’eed Hassan Jingir

Gamayyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) ta bayyana alhinin ta kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Sa’eed Hassan Jingir, mataimakin shugaban majalisar malamai na ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS), wanda ya rasu a safiyar Alhamis a Jos, bayan jinya mai tsawo.

Gamayyar ta kuma yi addu’ar Allah ya gafarta wa marigayin, ya karɓi kyawawan ayyukansa, ya ba shi Aljannatul Firdausi ga al’ummar Musulmi da ƙasa baki ɗaya, yana mai jaddada muhimmancin gudunmawar da marigayin ya bayar wajen yaɗa addini da kuma ƙarfafa zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna a cikin al’umma.

KU KUMA KARANTA:Allah Ya yi wa shahararren ɗan jarida, Malam Lawal Sa’idu Funtua rasuwa

Gwamna Yahaya ya ce, “Mun yi rashin babban malami mai daraja da kuma jagora. Hikimarsa da saƙonninsa na zaman lafiya, haɗin kai, da imani sun kasance abin koyi. Sadaukarwarsa ga haɗin kan al’umma da gagarumar iliminsa, tausayi, da hidima ba tare da son kai ba za su ci gaba da zama abin koyi ga al’ummar gaba.”

Gamayyar gwamnonin ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan marigayi Sheikh Jingir, shugabancin da mambobin JIBWIS, musamman shugaban majalisar malamai, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, da kuma daukacin al’ummar Musulmi.

Gamayyar ta kuma yi addu’ar Allah ya gafarta wa marigayin, ya karɓi kyawawan ayyukansa, ya ba shi Aljannatul Firdaus.

Marigayin ya rasu yana da shekaru 70, ya bar ‘ya’ya fiye da 40.

An kuma gudanar da jana’izarsa a ranar Alhamis, 6 ga Maris, 2025, inda dubban mutane daga ciki da wajen jihar suka halarta domin karramawa da yi masa addu’a.

Leave a Reply