‘Yansanda a Bauchi, sun cafke magidanci da ya lakada wa matarsa duka ta mutu har lahira

0
86
'Yansanda a Bauchi, sun cafke magidanci da ya lakada wa matarsa duka ta mutu har lahira

‘Yansanda a Bauchi, sun cafke magidanci da ya lakada wa matarsa duka ta mutu har lahira

Daga Ibraheem El-Tafseer

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wani mutum mai suna Alhaji Nuru Isah mai shekaru 50 bisa zarginsa da yin amfani da sanda wajen kashe matarsa ​​Wasila Abdullahi har lahira.

Lamarin ya faru ne a kusa da Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnati da ke unguwar Fadaman Mada a Bauchi.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Ahmed Wakil, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce, “A ranar 1 ga Maris, 2025, da misalin ƙarfe 11:30 na dare, rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta sanar da wani kisan gilla da ake zargin wani magidanci da aikatawa a kusa da Kwalejin ’yan mata ta gwamnati da ke unguwar Fadamam Mada, a Bauchi.

KU KUMA KARANTA:Dokoki 5 da masu wa’azi za su mayar da hankali kansu a watan Ramadan – Majalisar Malamai

“Wannan abin takaicin ya samo asali ne daga rashin fahimtar juna tsakanin wani magidanci Alhaji Nuru Isah mai shekaru 50, ɗan kasuwa a Central Market Bauchi da matarsa ​​ta biyu, Wasila Abdullahi mai shekaru 24, game da sarrafa kayan abincin buɗa baki da ‘ya’yan itatuwa da aka tanada domin shan ruwa na azumin watan Ramadan, wanda cece-kucen ya rikiɗe zuwa faɗa a tsakaninsu, wanda ta kai har ya mangare ta da sanda.”

Wakil ya ce bayan ya mangare matar ta sa da sandar ne ta faɗi, daga bisani aka kai ta asibitin koyarwa na ATBU, inda jami’an lafiya suka tabbatar da mutuwar ta.

Ya ce rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta fara gudanar da cikakken bincike kan lamarin, inda ya ce wanda ake zargin yana tsare.

Kwamishinan ‘yansanda, Auwal Musa Muhammad, ya tabbatar wa da jama’a cewa, tabbatar da adalci a shari’ar ya kasance muhimmin abin da rundunar ta sa gaba.

Leave a Reply