Dokoki 5 da masu wa’azi za su mayar da hankali kansu a watan Ramadan – Majalisar Malamai

0
43
Dokoki 5 da masu wa'azi za su mayar da hankali kansu a watan Ramadan - Majalisar Malamai

Dokoki 5 da masu wa’azi za su mayar da hankali kansu a watan Ramadan – Majalisar Malamai

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Shugaban majalisar malamai ta Arewancin Najeriya, Malam Ibrahim Khalil, ya ce abu ne mai kyau a duk lokacin azumin Ramadan, masu wa’azi su riƙa kallon yanayin da al’umma suka samu kansu a ciki, wanda hakan zai sa su mayar da hankali kansu a lokacin tafsirin karatun Alqur’ani.

KU KUMA KARANTA:Gobe Asabar za a fara Azumin watan Ramadan a Najeriya – Fadar Sarkin Musulmi

Malam Khalil ya ce a bana majalisar malamai na bukatar a mayar da hankali kan abubuwan biyar a yayin wa’azi.

1. Nunawa ‘yan ƙasa muhimmancin shugaba.

2. Sanyawa ‘yan ƙasa kishin ƙasar su.

3. Zaburar da shugabanni sannin nauyin da ke kansu

4. Nunawa ‘yan siyasa illar cin mutuncin juna a kafafen yaɗa labarai dama sauran shafukan sada zumunta.

5. Sai kuma su kansu Malaman su yiwa kansu faɗa domin gujewa yadda ‘yan siyasa ke amfani da su wajen cimma buƙatun su

Daga ƙarshe sun yi fatan wannan wata na Ramadan zai zama silar samun sauƙi da rangwame na matsi da al’ummar ƙasa ke ciki.

Leave a Reply